Sojoji sun hallaka mayakan Boko Haram/ISWAP da yawa a wani kwantan bauna a jahar Borno

Sojoji sun hallaka mayakan Boko Haram/ISWAP da yawa a wani kwantan bauna a jahar Borno

  • Dakarun sojin Operation Hadin Kai sun ragargaji mayakan kungiyar Boko Haram/ISWP a wani harin kwantan bauna a Borno
  • Rahoto ya nuna cewa aƙalla yan ta'adda hudu sojojin suka kashe, sannan kuma suka kwato muggan makamai daga hannun su
  • COAS Farouk Yahaya, ya yaba wa sojojin tare da ƙara musu kwarin guiwa su cigaba da hana yan ta'adda sakat a yankin

Borno - Dakarun sojin Operation Hadin Kai (OPHK) na bataliyar ta 82 sun yi wa mayakan ISWAP/Boko Haram mummunan ɓarna a yankun Pulka, jihar Borno.

Sojojin sun samu wannan nasara ne tare da taimakon jami'an sakai na JTF, da yan bijilanti bayan samun bayanan sirri.

Yayin kwantan bauna kan yan ta'addan, sojojin sun kashe mutum 4 tare da kwato muggan makamai da dama daga hannun su.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Dakarun Sojoji sun tarwatsa mayakan Boko Haram/ISWAP a kan hanyar Maiduguri

Sojoji
Sojoji sun hallaka mayakan Boko Haram/ISWAP da yawa a wani kwantan bauna a jahar Borno Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinta na Facebook, ɗauke da sa hannun kakakinta, Onyema Nwachukwu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nasarar dakarun soji a kwantan bauna

Bayan ragargazan yan ta'addan, wasu da dama daga cikin su, sun tsere da munanan raunuka dake zubar da jini a jikinsu.

Wani sashin sanarwan yace:

"Dakarun sojin sun kwato bindigun AK-47 guda uku, barkonon tsohuwa, gurneti da sauran makamai daga hannun yan ta'addan."

COAS ya yaba wa dakarun sojin

Da yake martani kan nasarar sojojin, babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya, ya roki sojojin su cigaba da irin haka, su hana yan ta'adda sakat a yankin.

Ya kuma kara wa sojojin kwarin guiwa kan irin wannan harin na kwantan bauna domin kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci a Arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13

Wannan na zuwa ne bayan wasu dakarun soji sun tarwatsa mayakan ISWAP da suka yi kokarin kai hari kan matafiya a hanyar Maiduguru.

A wani labarin na daban kuma Dubun wasu tsagerun yan bindiga da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara ya cika

Kwamandan rundunar NSCDC yace an gayyaci wani babban mutum wanda ake zargin yana da alaka da ɗaya daga cikin waɗanda aka kama.

Rahoto ya nuna cewa ɗaya daga cikin yan bindigan da aka kama ne ya fallasa sunan sanannen mutumin wanda ke ɗaukar nauyin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262