Kotu ta yanke wa ɗan Boko Haram hukuncin kisa ta hanyar rataya
- Wata babban kotu da ke zamanta a jihar Ekiti ta yanke wani dan kungiyar Boko Haram mai suna Abdulsalam Adinoyi hukuncin kisa ta hanyar rataya
- Kotun ta yanke hukuncin ne bayan wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa na fashi da makami, kisa, mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba da ta'addanci
- Adinoyi, wanda asalinsa dan garin Okene ne a jihar Kogi ya kashe wani dan sanda ya kuma yi musu fashi da ma wasu laifukan
Jihar Ekiti - Kotu ta yanke wa wani Abdulsalam Adinoyi, wanda ya amsa cewa shi dan Boko Haram ne hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa alkalin babban kotun jihar Ekiti, Lekan Ogunmoye ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba a Ado Ekiti.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An gurfanar da Mr Adinoyi a gaban kotun ne kan tuhuma biyar da suka hada da fashi da makami, kisa, ta'addanci da mallakar bindigu ba bisa ka'ida ba.
A hukuncin da ya bayar, Mr Ogunmoye ya ce masu gabatar da kara sun gamsar da kotu cewa wanda aka yi karar ya aikata laifukan da ake tuhumansa da su.
Tuhume-tuhumen
A cewar karar, Mr Adinoyi, wanda dan asalin Okene ne daga jihar Kogi, tsakanin ranar 22 ga watan Disambar 2016 da 20 ga watan Maris din 2017, ya yi amfani da bindiga ya yi wa Gana Jiya, dan sanda wasu abokan aikinsa fashi a Oye Ekiti.
Ya kashe Mr Jiya a wurin yayin da ya raunata sauran yan sandan da bindiga kamar yadda ya zo a ruwayar ta Premium Times.
An zarge shi da sace bindiga AK-47 biyu tare da kai hare-haren ta'addanci ga mutanen Ekiti da kewaye.
Ya amsa cewa shi dan ta'adda ne
Mr Adinoyi ya amsa cewa shi dan ta'adda ne kuma ya mallaki bindiga AK-47.
Ya kuma amsa cewa shi da yan kungiyarsu, Abu Uwais da Aminu aka Idi-Amin da yanzu ake namansu, suna shirin kai hari ofishin yan sanda ne a lokacin da yan sanda suka zo gidansa, inda suka bincika suka gano AK-47 da wasu makamai.
Laifukan da Mr Adinoyi ya aikata sun ci karo da sashi na 1 (2) (a) and 3(1) na dokar fashi da makami da wasu sassan dokokin da ke kudin tsarin Nigeria da jihar Ekiti.
"An samu wanda ake zargin da laifin da aka tuhume shi, don haka an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya kan tuhuma 1, 2 da 3. Allah ya yi masa rahama.
"An kuma yanke masa daurin shekaru 20 kan tuhuma ta 4 da shekaru goma kan tuhuma ta 5 da zabin biyan tara ta N10,000.00," a cewar alkalin.
An kashe Dogo Giɗe, ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya daɗe yana addabar jihohin arewa
A baya, Legit ta kawo muku wani rahoto da ya ce an kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga Dogo Gide.
An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna kamar yadda PRNigeria ta wallafa.
A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin.
Asali: Legit.ng