Dalilai 2 da suka sa Shugaban Kasa Buhari yake jin haushin Sheikh Ahmad Gumi inji Mamu

Dalilai 2 da suka sa Shugaban Kasa Buhari yake jin haushin Sheikh Ahmad Gumi inji Mamu

  • Alhaji Tukur Mamu ya bayyana alakar shugaban kasa da Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.
  • Mai magana da yawun Dr. Ahmad Gumi yace mutane suna yi wa shehin wata mummunar fassara.
  • Mamu yace Buhari ya samu sabani da Gumi ne saboda ya bada shawarar kar ya je kotu a zaben 2007.

Kaduna - Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi suna a matsayin malamin addini, kuma mai kokarin kawo zaman lafiya a Arewacin Najeriya.

Vanguard tayi hira da Tukur Mamu wanda shi ne mai magana da yawun bakin Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, domin ya fitar da mutane daga duhu.

Alhaji Tukur Mamu yace sam mutane ba su fahimci Dr. Gumi ba, kuma ba ya goyon bayan ‘yan bindiga, sai dai ma rubutunsa yana nuna akasin hakan.

Mamu yace Shehin malamin yana ganin cewa akwai bambanci tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram, don haka ya kamata a zo masu da salo dabam.

Kara karanta wannan

Bidiyon Maina yana dariya a kotu bayan yanke masa ɗaurin shekaru 8 a gidan yari ya janyo cece-kuce

An tambayi Mamu ko me ya hana Ahmad Gumi ya zauna da shugaban kasa ko masu rike da madafan iko domin a shawo kan matsalar rashin tsaro.

Dalilai 2 da suka sa Shugaban Kasa Buhari yake jin haushin Sheikh Ahmad Gumi inji Mamu
Sheikh Ahmad Gumi
Asali: Facebook

Wace amsa Tukur Mamu ya bada?

“Mun yi kokarin mu zauna da shugaban kasa daga mu sai shi; kun san shugaban kasa mutum ne da yake ajiye abu a cikin ransa.” – Tukur Mamu.
Matsalar da Dr. Gumi ya fara samu da shugaban kasa tun lokacin ‘Yar’adua ne. Gumi ya zauna da su, ya bada shawarar a hakura shigar da kara a kotu.”
“Na halarci taron, Gumi ya bada shawarar su hakura da kai kara tun da ‘Yar’adua ya yarda cewa akwai matsala a harkar zabe, kuma zai kawo gyara."

Me ya jawo sabani na biyu?

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

A cewar Mamu, duk da haka sai Buhari ya shigar da kara a kotu, daga nan suka soma samun matsala.

Matsala ta biyu ita ce a 2015, a lokacin da Dr. Gumi yace Buhari da Jonathan duk ba su cancanci suyi mulki ba, su bar masu kananan shekaru su yi takara.

Wadannan abubuwa suka batawa Buhari rai, sannan Mamu yace sun nemi izinin hukumomi kafin su fara shiga jeji, amma shugaban kasan bai amince ba.

Buhari ya bar Najeriya

A jiya ne aka ji Muhammadu Buhari ya isa birnin Faris, inda Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai ba shi masauki a fadar Shugaban kasa.

Shugaba Macron, Kamala Harris, da Buhari duk za su yi jawabi a gaban manyan Duniya a taron zaman lafiya da za a fara a ranar Alhamis dinnan.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta hukunta mutane sama da 1, 000 da suka saba doka

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng