Rushewar Ginin Legas: Sun hanani aiki a wajen don ni Musulmi ne, bayan awa biyu ginin ya rushe

Rushewar Ginin Legas: Sun hanani aiki a wajen don ni Musulmi ne, bayan awa biyu ginin ya rushe

  • Wani Matashi ya bayyana abinda ya faru da shi ranar da gini mai hawa 21 ya rufto kan mutane a unguwar jihar Legas
  • Matashin ya bayyana yadda aka ki bashi aiki a wajen ranan saboda shi Musulmi ne kuma yana Sallah
  • Kawo yanzu an ciro gawawwakin mutum 43 da ginn ya rufta da su yayinda wasu suka tsallake rijiya da baya

Legas - Wani Injiniya mai suna Sikiru Adebowale ya bayyana yadda Allah ya tsiratar da shi daga rushewar gini mai hawa 21 da ya auku a Legas ranar 2 ga Nuwamba, 2021.

Injinyan ya bayyana cewa ginin ya rufto kan dukkan wadanda ke ciki kimanin sa'o'i biyu bayan da ya bar wajen.

Ya ce Mai ginin ya fitittikesa ne saboda kawai shi Musulmi ne kuma ba zai iya daukan mai kiran sunan Allah a wajen aikinsa ba.

Kara karanta wannan

Makiyaya sun miƙa wa ƴan sanda ɗan uwansu, Jabir Nuhu, bayan ya kashe manomi

Sikiru wanda mazaunin jihar Legas ne ya bayyana hakan a hirar da yayi da AN24 Tv kwana daya bayan aukuwan lamarin.

A cewarsa:

"Na tafi intabiu ne da shugaban Foursquare Mr Femi don yin aikin Injiniya a wajen. Lokacin intabiun na yi masa bayanin irin ayyukan da nayi a baya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Da farko sai ya tambayeni, wani Coci nike zuwa, sai nace masa ni Musulmi ne. Sai yace, 'Sam ba zan iya aiki da Musulmi ba.' Ban ji dadi ba, bai kamata addini na ya shafi aikin da zan yi ko iyawa na ba."
"Sai ya fadi da yaren Yarbanci 'Idan kana gidana yanzu sai kace za kayi Sallah? Ko zaka rika kiran Alhamdulillah a ginin?'."

Rushewar Ginin Legas
Rushewar Ginin Legas: Sun hanani aiki a wajen don ni Musulmi ne, bayan awa biyu ginin ya rushe Hoto: AN24 Tv
Asali: Facebook

Yace kila don ni Musulmi ne yasa ban samu cigaba a rayuwa ba

Kara karanta wannan

'Dan sanda ya daɓa wa abokin aikinsa wuƙa ya yi sanadin ajalinsa

Sikiru ya bayyana cewa maimakon ko da baya son Musulmi, yayi kokarin fada masa a kaikaice cewa ba zai daukesa aiki ba, amma ya fito fili ya bayyana cewa ba zai dauki Musulmi ba.

Yace:

"Na yi masa bayanin wahalhalun da na sha a baya, nayi aiki a gona, lokacin da na gama makaranta da sauransu, sai yace kila don addini na ne yasa ban samu cigaba a rayuwa ba. Kuma a gaban kowa ya fadi hakan, leburori, birkiloli."

Ina hanyar tafiya gida abokina ya kirani

A hirar, Sikiru yace ba tare da bata lokaci ba ya bar wajen kuma ya kama hanyarsa ta tafiya gida.

Yayinda yake hanyar tafiya gida sai ya yada zango wajen abokinsa don ya wuce fushin abinda ya fuskanta.

Yace:

"Kawai sai abokina ya kira yana tambayana ina nake, yace min shin na samu labarin abinda ke faruwa game da ginin kuwa, ginin fa ya rushe."

Kara karanta wannan

Mai kudin duniya ya yi alkawarin bada kyautar $6bn idan akayi masa bayanin yadda za'a kashe

"Da muke duba Instablog, sai naga daidai inda muka zauna ya rushe. Abin bai min dadi ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: