Paris Club: Minista, Gwamnoni na rigima kan biliyoyin da aka biya masana daga asusunsu
- Gwamnoni sun samu sabani da Gwamnatin tarayya a kan wasu kudi da aka cire daga bashin Paris Club.
- Minista shari’a, AGF ya zaftare $418m (fiye da N170bn) daga asusun jihohi da kananan hukumomi.
- Kungiyar NGF tace Abubakar Malami bai da hurumin da zai cire masu wadannan makudan biliyoyi.
Abuja - Kungiyar gwamnonin Najeriya ta zargi Ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN da saba doka wajen cire kaso maso tsoka daga bashin Paris Club.
Jaridar Punch tace gwamnoni na zargin Abubakar Malami da biyan masu bada shawara $418m, wanda suka ce hakan ba daidai bane, kuma ya saba doka.
Abdulrazaque Bello-Barkindo wanda shi ne shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar ya sa hannu a jawabin, a madadin gwamnoni 36.
Jaridar Daily Trust tace gwamnonin sun ce ba daidai ba ne a dauki kason jihohi da kananan hukumomi daga kudin Paris Club, a biya masu bada shawara.
Abdulrazaque Bello-Barkindo ya fitar da jawabi
Da yake magana a ranar Litinin, Malam Abdulrazaque Bello-Barkindo yace biliyoyin da ake shirin biyan kamfanonin LINTAS da NED Nwoko abin dubawa ne.
“LINTAS da NED Nwoko za su tashi da fam US$68,658,193.83 daga kudin jihohi na aikin bada shawarar da suka yi.” - Abdulrazaque Bello-Barkindo.
“Shin AGF bai da labarin aikin da aka ce an yi yana cikin rahoton kwamitin sulhu na FAAC da aka gabatar a 2005 kan yadda za a biya bashin Paris Club?”
PANIC Alert Security Systems Ltd ya ci $418m?
Kungiyar gwamnonin ta koka a kan Dala miliyan $47.8 da aka biya kamfanin PANIC Alert Security Systems Ltd da George Uboh da sunan sun yi wani aiki.
Bello-Barkindo ya bukaci Ministan shari’a ya nuna inda aka bada dama gwamnati ta biya kamfanin wadannan kudi, yace dole ya yi wa al’umma bayani.
Jihohi 33 suna cikin matsala
NGF ta yi tir da yadda Malami yake gaggawar zaftare wadannan kudi, a lokacin da wasu batutuwan da suka dade suke kotu, har yanzu, ba a dabbaka su ba.
Rahoton yace idan aka yi wa kason jihohi gibi a asusun FAAC, jihohi 33 ba za su iya biyan albashi ba.
Asali: Legit.ng