Bidiyon Ango Yana Sharɓar Kuka a Yayin Da Iyayensa Da Surukansa Suka Raka Shi Ɗakin Amarya

Bidiyon Ango Yana Sharɓar Kuka a Yayin Da Iyayensa Da Surukansa Suka Raka Shi Ɗakin Amarya

  • Wani ango ya kasa rike murnar da ke zuciyarsa har ta kai ga sai da yan uwansa da surukansa suka taimaka masa kafin shiga dakin amarya
  • A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, an gano angon iyayensa da surukansa sun masa rakiya zuwa dakin amaryarsa
  • Angon mai cike da kunya ya fara yin musabaha da matarsa sannan daga baya ya fara zubar da hawaye bayan ya hau babban gadon da ta ke

Lamarin aure batu ne da ke tsakanin mata da miji amma wani ango ya kasa zuwa dakin amaryarsa har sai da iyayensa da surukansa suka yi masa rakiya har kan gado.

Kuma angon ya yi abubuwa masu ban dariya yayin da aka yi masa rakiyar lamarin dai kamar dirama.

Bidiyon Ango Yana Sharɓar Kuka a Yayin Da Iyayensa Da Surukansa Suka Raka Shi Ɗakin Amarya
Bidiyon Ango Yana Kuka a Yayin Da Iyayensa Da Surukansa Suka Raka Shi Ɗakin Amarya. Hoto: @wisdomblogg
Asali: Instagram

A wani gajeren bidiyo da Wisdom Blog ya wallafa, angon tare da surukansa da 'yan uwansa sun shigo dakin amaryar da wayoyinsu domin daukan yadda haduwan farkon zai kasance.

Kara karanta wannan

Makiyaya sun miƙa wa ƴan sanda ɗan uwansu, Jabir Nuhu, bayan ya kashe manomi

A wani lamari mai kama da aure na musulmi, angon ya fara yin musabaha da amaryarsa wacce ke zaune kan gado cikin addo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga bisani ya zauna kusa da amaryarsa wacce ko gezau ba ta yi ba yayin da wani malami ke musu addu'o'i.

Bayan kammala addu'o'in, angon ya fashe da kuka.

Ma'abota amfani da shafukan sadarwa sun tofa albarkacin bakinsu

@humbetee ya ce:

"Haha, me yasa wannan abin ya bani dariya, mene ya ke yi wa kuka?"

ita kuma @timcee_o cewa ta yi:

"Hahahaha sai su dage su koya masa abinda zai biyo baya kuma."

@innenane ta ce:

"Bisa ga dukkan alamu wannan bai saba da harkokin aure ba kuma yana da kunya ... amma amaryar idon ta bude ido."

@freedah_accessories cewa ta yi:

"Me yasa ya ke kuka."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164