Gwamnan Ondo ya yi koyi da Gwamna El-Rufai, ya yi karin 120% a kudin makarantar Jami'a
- Jam’iyyar hamayya ta PDP ta soki karin kudin makarantar da gwamnatin Rotimi Akeredolu ta yi.
- Sakataren yada labaran PDP a jihar Ondo ya fitar da jawabi, yana cewa iyaye za su cire ‘ya ‘yansu.
- Kennedy Peretei yace karin 120% da aka yi a kudin karatun jami’ar UNIMED zai jefa iyaye matsala.
Ondo - Jam’iyyar hamayya ta PDP ta reshen jihar Ondo ta yi Allah-wadai da karin kudin makarantar da gwamnatin Rotimi Akeredolu tayi.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jam’iyyar PDP ta soki matakin da aka dauka na kara kudin karatu a jami’ar koyar da ilmin likitanci watau UNIMED.
PDP tace Rotimi Akeredolu ba tayi tunani wajen daukar wannan mataki ba, sannan tace hakan zai sa a samu yara da-dama da ba su zuwa makaranta.
Kennedy Peretei ya fitar da jawabi
Sakataren yada labarai na PDP a jihar Ondo, Kennedy Peretei ya fitar da jawabi a karshen makon nan, yace karin na 120% zai jefa iyaye cikin wahala.
Kennedy Peretei yace wannan karin tashin hankalin da gwamnatin jihar Ondo tayi yana nufin iyaye su cire ‘ya ‘yansu daga wannan jami’a ta UNIMED.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Karin kudin makarantar gauron zabin da gwamnatin Ondo tayi wa daliban jami’ar jiha ta UNIMED na jihar Ondo kira ne ga iyayen da ba su iya biyan kudin ba da su cire ‘ya ‘yansu.” – PDP.
Rotimi Akeredolu SAN bai taba boye niyyarsa na kara kudin karatu a makarantun gwamnatin jihar Ondo ba tun da ya zama gwamna.”
Ba yau aka saba ba - PDP
"An yi zanga-zanga a makarantun Adekunle Ajasin, Akungba Akoko da jami’ar kimiyya ta Olusegun Agagu da ke Okitipupa saboda karin kudi."
"Adadin daliban Rufus Giwa Polytechnic, Owo ya ragu daga 9,000 zuwa 1,753 saboda karin kudi." - PDP.
A cewar Kennedy Peretei, mafi yawan gidajen garin Owo sun washe, tattalin arzikin garin ya ruguje saboda daliban da ke karatu sun bar makarantar.
Kungiyar AYCF ta yi magana a kan zaben 2023
Dazu aka ji cewa Kungiyar AYCF ta matasan Arewa tace babu ruwanta da ‘Dan takarar da ya haura shekara 60 a zaben shugaban kasan da za ayi a 2023.
Shugaban kungiyar yace ba za su goyi bayan dattijon 'dan takara ba. Irinsu Gwamna Yahaya Bello da Aminu Tambuwal ne ba za su haura shekara 60 a 2023 ba.
Asali: Legit.ng