Kotu ta yanke wa Maina hukuncin shekaru 8 a gidan yari bayan kama shi da laifin satar N2b
- Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kama tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, da laifin satar kudi har N2 biliyan
- Mai shari'a Okong Abang, ya yanke cewa kotu ta kama Maina da laifin handamar kudi har biliyan 2 na 'yan fansho
- Mai shari'a Okon Abang na babbar kotun ya yanke wa Maina hukuncin zaman shekaru 8 a gidan gyaran hali
Babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin ta kama tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, Abdulrasheed Maina, da laifin sata da wanke kudin haram zuwa na halas, Premium Times ta ruwaito.
A wani hukunci da Okong Abang, alkalin kotun ya yanke, ya ce kotun ta kama Maina da laifin satar kudi sama da biliyan 2 na 'yan fansho "wadanda da yawansu sun rasu kuma basu ci guminsu ba," alkalin yace.
"Na kama Maina da laifin aikata zargi na 2, 6, 9, 3, 7 da na 10," Abang yace.
Mais shari'a Abang ya yanke wa Abdulrasheed hukuncin shekaru takwas a gidan gyaran hali.
A wata daya da ya gabata, kotu ta daure Faisal Maina, wanda ta kama shi da laifuka ukun da aka zargesa da su wadanda suka hada da halasta kudin haram har N58.1 miliyan.
Har a halin yanzu, babu rahoton cewa Faisal ya na gidan gyaran hali, Premium Times ta wallafa.
Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da Maina a gaban Abang a ranar 25 ga watan Oktoba 2019 da kamfanin Common Input Property and Investment Ltd.
An gurfanar da Maina ne kan laifuka 12 da ake zarginsa da su.
Daga cikin zargin da ake wa Maina akwai yin amfani da kamfaninsa domin boye kudin sata har N2 biliyan kuma ya yi amfani da su wurin siyan kadarori a Abuja.
Maina ya musanta aikata wadannan laifukan.
Kotu ta janye belin Faisal Maina, ta bukaci a damko shi
A wani labari na daban, a ranar Talata, babbar kotun tarayya ta Abuja, ta umarci a kama yaron tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, Faisal, bayan kin bayyanarsa a kotu don a cigaba da shari'a a kan zargin ha'inci da ake masa.
Alkali mai shari'a, Okon Abang, ya umarci jami'an tsaro da su kama Faisal duk inda suka gan shi. Kotun ta gayyaci wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaura-Namoda, Umar Galadima, don ya bayyana a gabanta ranar Laraba.
Kotun ta umarci ya bayyana don ya bayar da hojojin da za su hana a kulle shi ko kuma ya biya naira miliyan 60 na beli ga gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng