Mohammed Sani Abacha ya fallasa kansa, ya bayyana yadda suka mallaki rijiyar mai
- Mohammed Abacha yace ya yi amfani da sunan Mohammed Sani ne domin samun rijiyar OPL 245.
- Babban yaron tsohon shugaba Sani Abacha ya bayyana haka ne da aka wata shari’a da shi a kotu.
- ‘Dan siyasar yace an cire sunansa daga kamfanin Malabu Oil and Gas a lokacin da yake kurkuku.
Abuja - Mohammed Abacha ya yi magana a gaban babban kotun tarayya, inda ya bayyana yadda ya yi amfani da wani suna domin ya mallaki rijiyar mai.
The Cable ta kawo rahoto cewa Abacha ya fadawa Alkali cewa ya yi amfani sunan Mohammed Sani wajen yi wa kamfanin Malabu Oil and Gas rajista.
A shekarar 1998 ne aka ba Malabu Oil and Gas Ltd rijiyar man OPL 245 da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Da farko Mohammed Sani (Abacha) ne yake da 50% na hannun jarin kamfanin Malabu Oil and Gas Ltd, Kweku Amafegha ya mallaki 30% na hannun jarin.
An fi sanin Kweku Amafegha da Dan Etete, wanda shi ne Ministan harkokin mai na Najeriya a lokacin da aka ba kamfanin na Malabu Oil & Gas rijiyar.
Wabi Hassan, matar Jakadan Najeriya a kasar Amurka a lokacin, Hassan Adamu, take da ragowar wannan jarin wannan kamfani da ake ta shari’a da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda aka kare da rijiyar OPL 245
A lokacin da wannan abin ya faru, marigayi Janar Sani Abacha ne shugaban kasa. Alhaji Mohammed Abacha yana cikin ‘ya ‘yan tsohon shugaban.
Da Olusegun Obasanjo ya zama shugaban kasa, ya soke yarjejeniyar rijiyar man a 2001. Amma a karshe kotu ta sake maidawa kamfanin bayan an yi shari’a.
A karshe Malabu Oil and Gas sun saida rijiyar ga kamfanin Shell and Eni a kan fam Dala biliyan 1.1, baya ga wasu kudi da aka damkawa gwamnatin Najeriya.
Jami’in EFCC, Bala Sanga ya gabatar da Abacha a matsayin shaida a gaban Alkali Abubakar Kutigi.
Abacha ya shaidawa kotu cewa a lokacin da yake tsare tsakanin 1999 da 2002, an cire sunan shi daga cikin masu hannun jari a wannan kamfani na Malabu.
Rajneesh Narula ya zama mai ba gwamnati shawara
A jiya aka ji Farfesa Rajneesh Narula ya zama mai ba gwamnatin jihar Kaduna shawara a kan tsare-tsaren manufofi. Farfesan yana cikin masanan Duniya.
Farfesa Rajneesh Narula ya fara karatunsa da aiki ne a Najeriya, daga nan ya wuce kasar Birtaniya inda ya yi digirgir a MBA da PhD a harkar tattali.
Asali: Legit.ng