Da duminsa: IGP ya bukaci sunayen 'yan sandan da har yanzu ba a biya ba a Anambra
- Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya umarci a bada sunayen 'yan sandan da basu samu kudin aikin zabensu ba a Anambra
- Kamar yadda mai magana da yawun rundunar, Frank Mba ya bayyana, an samu tsaikon ne sakamakon matsalar bayanan banki da aka samu
- Frank Mba ya sanar da cewa, a cikin jami'ai dubu talatin, a halin yanzu an biya dubu ashirin da tara kudin aikinsu tun kafin ranar zaben
Anambra - Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya umarci dukkan kwamandoji da su tattaro sunayen 'yan sandan da ke aikin zabe a Anambra kuma ba a biya su ba har yanzu.
Wannan ya biyo bayan korafin da wasu 'yan sanda suka yi kan cewa ba a biya su kudin alawus na zaben gwamnan Anambra ba, Daily Trust ta wallafa.
Daily Trust ta ruwaito yadda wani dan sanda da ke aiki da rumfar zabe ta takwas a gunduma ta biyu da ke Abagana, karamar hukumar Njikoka ta jihar Anambra, ya koka da rashin abinci yayin zaben.
Sama da 'yan sanda dubu talatin aka tura domin zaben jihar Anambra wanda ake yi a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.
A wata tattaunawa da cibiyar habaka damokaradiyya, CDD ta yi a ranar Asabar, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda, Frank Mba, ya ce Sifeta janar na 'yan sanda ya alakanta rashin biyan da bayanan banki wadanda aka bayar ba daidai ba.
Mba ya ce sama da jami'ai dubu 29 ne aka rubuta sunayensu da bayanansu kuma suka samu kudadensu.
"Sifeta janar tuni ya bayar da umarni da ranan yau ga kwamandoji da su tattaro sunayen 'yan sanda da basu samu kudin zabensu ba."
“Wannan ne karo na farko da muka fara biyan kudin ma'aikata kafin a yi zabe," yace.
Zaben Anambra: Babu abinci, dan sanda ya koka kan yunwar da ta addabe shi
A wani labari na daban, a yanzu haka ana nan ana ci gaba da gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra a yau Asabar, 6 ga watan Nuwamba.
Yayin da zaben ke gudana, wani jami'in dan sanda da ke aiki a rumfar zabe ta PU8, Abagana ward 2, karamar hukumar Njikoka, ya koka a kan yunwar da ta addabe shi.
Jami'in tsaron wanda aka boye sunansa ya bayyana cewa babu wani tanadi da aka yi masu na abinci, Jaridar Daily Trust ta rahoto. An kuma tattaro cewa dan sandan shine ya taimakawa jami'an zabe a lokacin da ake tantancewa da gudanar da zaben.
Asali: Legit.ng