Majalisar Najeriya ta ba Buhari awa 24 rak ya ayyana ‘Yan bindiga a sahun ‘Yan ta’adda
- Kwamitin da ke lura da sojojin kasa a majalisar tarayya ta ba shugaba Muhammadu Buhari wa’adi.
- Honarabul Abdulrazak Namdas ya bukaci a ayyana ‘yan bindiga a cikin sahun ‘yan ta’adda a Najeriya.
- Hon. Namdas a madadin Majalisar wakilan tarayya yana so gwamnati tayi wannan cikin sa’a 24
FCT, Abuja - Kwamitin harkar sojojin kasa na majalisar wakilan tarayya ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya dauki mataki a kan ‘yan bindiga.
Jaridar Punch tace ‘yan majalisar tarayyar suna so shugaban kasa ya ayyana wadannan miyagun ‘yan bindiga a cikin ‘yan ta’addan da suka addabi Najeriya.
Shugaban wannan kwamiti, Abdulrazak Namdas ya yi wannan kira da shugaban hafsun soja, Laftanan Janar Farouk Yahaya ya bayyana a gabansu jiya.
Janar Farouk Yahaya ya ziyarci majalisa ne domin ya kare kasafin gidan sojan kasa a ranar Juma’a.
Honarabul Abdulrazak Namdas yana so a dauki wannan mataki nan da sa’a 24. ‘Dan majaliar yace hakan zai taimakawa sojojin wajen murkushe miyagun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abin ya fara yawa - Abdulrazak Namdas
A jawabin da Abdulrazak Namdas, yace ta’adin wadannan ‘yan bindiga yana nema ya yi yawa.
“Majalisar tarayya – Sanatoci da ‘yan majalisa sun dauki matsayan kira ga shugaban kasa ya ayyana ‘yan bindiga cikin ‘yan ta’adda.”- Namdas.
“Saboda sojoji su dumfari wannan kalubale, ayi ta ta kare. Mun san cewa yanzu ana fama da matsalolin amfani da makamai saboda wani yanayi.”
“Muna bukatar shugaban kasa ya taimaka ya sa hannu, saboda sha’anin ‘yan bindigan nan yana kara wahala, ya fi abin da aka yi a arewa maso gabas.”
Namdas yana fatan idan an kammala aiki a kan kudirin tallafawa sojojin kasa, ya kuma kai zuwa fadar shugaban kasa, za a shawo kan matsalar rashin tsaro.
Majalisa ta hurowa Rotimi Amaechi wuta
A karshen makon nan aka ji Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana gaban majalisar tarayya inda ya kare kasafin kudin ma'aikatarsa na shekarar 2022.
Gwamnatin Tarayya tana shirin kashe makudan kudi wajen gina titin jirgi zuwa Maradi. Sanatoci da ‘Yan majalisa sun ce akwai son kai a aikin da Amaechi yake yi
Asali: Legit.ng