Da Dumi-Dumi: Mamallakin dogon gini mai hawa 21 da ya rushe a Legas ya mutu

Da Dumi-Dumi: Mamallakin dogon gini mai hawa 21 da ya rushe a Legas ya mutu

  • Rahotanni daga wurin aikin ceto na dogon gini mai hawa 21 da ya rushe a Legas, sun nuna cewa an gano gawar mamallakin ginin
  • Femi Osibona, wanda shine shugaban kamfanin Fourscore Homes Limited, ya rasa ransa a ginin kamfanin nasa
  • A halin yanzun an ceto mutum 9 da ransu, yayin da aka gano gawarwakin mutane sama da 30

Lagos - Shugaban kamfanin Fourscore Homes Limited, mai suna, Femi Osibona, ya rigamu gidan gaskiya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Osibona shine mamallakin kamfanin da yake gina dogon gini mai hawa 21, wanda ya kife a Ikoyi, jihar Lagos ranar Litinin.

Ma'aikatan dake aikin ceto a wurin, sun shaida wa jaridar cewa mintuna kaɗan da suka shuɗe aka gano gawar mutumin.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ƙungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zaɓe a Anambra

Ginin Legas
Da Dumi-Dumi: Mamallakin dogon gini mai hawa 21 da ya rushe a Legas ya mutu Hoto: myjoyonline.com
Asali: UGC

An shiga damuwa bisa rashin gano Osibona, da kuma wani abokinsa, Wale Bob-Oseni, da wasu mutane waɗanda ake da tabbacin ginin ya kife da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bob-Oseni, wanda ke kan hanyar zuwa ya hau jirgi domin tafiya Amurka, ya biya ta wurin ginin domin ganin yadda aiki ke tafiya, amma bai fito a raye ba.

Yayin da ake cigaba da aikin binciko waɗan da lamarin ya rutsa da su, an ceto mutum 9, sama da 30 kuma an tabbatar da sun mutu.

NEMA ta tabbatar da lamarin

Hukumar bada agajin gaggaawa ta ƙasa (NEMA) ta tabbatar da gano gawar Osibona, ga jaridar The Cable da yammacin ranar Alhamis.

A ranar Alhamis da dare an samu ƙarin jami'an tsaro a wurin ginin, yayin da ma'aikatan lafiya suka ɗauki gawarsa.

Har yanzun babu tabbacin adadin mutanen dake cikin ginin a lokacin ya rushe, ya rufe mutanen a ciki.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon rushewar gini a Legas ya karu zuwa 36

A wani labarin kuma Dakarun soji sun fice sun bar yan sanda da aikin tsaro a jihar Ondo ba tare da bayyana dalili ba

Tuni hukumar yan sanda ta jibge jami'an ta a waɗan nan wuraren da sojoji suka tashi, domin cigaba da kare al'umma.

Wannan lamari ya jawo musayar yawu tsakanin gwamnatin jihar da kuma babbar jam'iyyar hamayya PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: