Hotunan jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki

Hotunan jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki

  • Babu shakka jama'a masu yawa za su yi zaton jami'o'in farko na duniya an kafa su a Turai ne, sai dai ba haka ba ne
  • Jami'o'i hudu kuwa da aka fara kafawa a duniya duk a Afrika ne kuma daya daga ciki mace ce ta kafa ta
  • Akwai jami'ar farko a kasar Tunisia, ta biyu a kasar Morocco, ta uku kuwa a kasar Misra yayin da ta hudu a kasar Mali

Afrika - Jama'a masu yawa sun yi zaton tsofaffin jami'o'i na duniya za su kasance a Turai. Amma kuma ba hakan ba ne, Afrika ita ce nahiyar da aka fara samun jami'o'i hudu masu dadewa kuma daya daga cikinsu mace ce ta samar da ita.

Legit.ng ta gabatar muku da tsoffin jami'o'in duniya kamar yadda Erudera ta bayyana.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da mijin da ya soka wa matarsa almakashi, ta sheka lahira

1. Jami'ar Ez-Zitouna ta kasar Tunisia

Jami'ar Ez-Zitouna da ke kasar Tunisia ita ce jami'a mafi dadewa a duniya da har yanzu ta ke aiki. An kafa jami'ar a shekarar 737 a matsayin Madrasa kafin daga bisani ta zama jami'a.

Daliban makarantar nan na iya samun ilimi a bangaren kimiyya, falsafa, lissafi, zane da sauransu. Jami'ar ta ga lokuta daban-daban na yaki wanda kuma sun wuce sun bar ta.

Jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki
Jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki. Hoto daga Qantara.de
Asali: UGC

2. Jami'ar Al-Qarawiyyin da ke kasar Morocco

An kafa jami'ar kasar Moroccon a shekarar 859 AD wanda wata mata mai suna Fatima Al-Fihri ta kafa.

Ta yi amfani da kudin da ta gada daga mahaifin ta wurin gina masallacin Al-Qarawiyyin, wanda daga bisani aka mayar da shi cibiyar ilimi inda daga baya ya zama jami'ar A-Qarawiyyin.

Kara karanta wannan

'Yan dadi Afrika: Yadda mata 3 suka bar kasashensu na turai suka kauro Afrika, Najeriya

Jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki
Jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki. Hoto daga DeAgostin
Asali: Getty Images

3. Jami'ar Al-Azhar da ke Misra

Jami'ar Al-Azhar wacce ke Cairo, an kafa ta ne tun a shekarar 970 AD. Kamar yadda CSIA, jami'ar Al-Azhar ta na samun dalibai a kalla dubu talatin daga kasashe dari na duniya.

Jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki
Jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki. Hoto daga Universal History Archive
Asali: Getty Images

4. Masallacin Sankore da jami'a da ke kasar Mali

Kamar yadda Erudera ta wallafa, wannan tsangayar Mansa Musa ne ya samar da ita tun a shekarar 989, wanda ake kwatanta shi da mutumin da ya fi kowa arziki wanda ya rayu a tarihin duniya.

Jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki
Jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki. Hoto daga Wolfgang Kaehler/LightRocket
Asali: Getty Images

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng