Yanzu-yanzu: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon rushewar gini a Legas ya karu zuwa 36

Yanzu-yanzu: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon rushewar gini a Legas ya karu zuwa 36

  • Adadin mutanen da suka rasu sakamakon rushewar gini mai hawa 21 a unguwar Ikoyi na jihar Legas ya tashi daga 22 ya kai 36
  • Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ziyarci wurin da abin ya faru inda ya ce an kafa kwamitin bincike don gano abin da ya yi sanadin rushewar
  • Sanwo-Olu ya kuma bada tabbacin cewa tabbas za a hukunta dukkan wadanda aka same su da hannu wurin rushewar ginin

Jihar Legas - Adadin mutanen da suka rasu sakamakon rushewar gini a unguwar Ikoyi, jihar Legas a ranar Litinin ya tashi daga 22 ya kai 36.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa daga cikin 36 da suka rasu kawo yanzu, uku daga cikinsu mata ne sai kuma maza 33.

Yanzu-yanzu: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon rushewar gini a Legas ya kai 36
Yanzu-yanzu: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon rushewar gini a Legas ya kai 36
Asali: UGC

Shugaban hukumar bada agajin gaggaw ana kasa, NEMA, na kudu maso yamma, Ibrahim Farinloye, ne ya bada sanarwar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hoton karshe na ginin da ya rubto a Legas: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da wannan gini

Ya kuma ce cikin mutum 9 da aka ceto, daya mace ne yayin da sauran 8 maza ne.

Ya kara da cewa:

"Daga cikin wadanda aka ceto, muna da mace daya sai kuma maza takwas. Cikin wadanda suka rasu, akwai mata uku sannan maza guda 33.
"Ana cigaba da aikin ceton rai kuma mun samu karin masu bada gudunmawa."

Ginin da ake yi a Gerrard road da ke yankin highbrow a Legas ya rushe ne a ranar Litinin, inda mai ginin da wasu ma'aikata suka makale.

Ana cigaba da aikin ceton mutanen da ginin mai hawa 21 ya fado musu tun a ranar Litinin da rana.

Iyalai da abokan mutanen da abin ya faru da su sun kwana a wurin suna addu'a da fatan a ceto yan uwansu da ransu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mamallakin dogon gini mai hawa 21 da ya rushe a Legas ya mutu

Gwamna Sanwo-Olu ya ziyarci wurin da ginin ya rushe

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ce adadin wadanda suka rasu sun kai 21 a ranar Laraba.

Kawo yanzu ba a tabbatar da ainihin abin da ya yi sanadin rushewar ginin ba, amma gwamnan ya ce akwai alamun cewa an saba dokoki da kurakurai.

Tuni da ya kafa kwamitin bincike kan afkuwar lamarin ya kuma yi alkawarin cewa za a hukunta dukkan wadanda aka samu da laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: