Rikici ya barke tsakanin Jaruma Mai Kayan Mata da matar Biloniya, Regina Daniels

Rikici ya barke tsakanin Jaruma Mai Kayan Mata da matar Biloniya, Regina Daniels

  • Dillaliyar kayan mata, Jaruma Empire, ta caccaki kawarta, jarumar Nollywood kuma matar Biloniya, Regina Daniels
  • Jaruma ta zazzagewa Regina Daniels inda ta bayyana dukkan abubuwan da suka faru tsakaninsu na kudi
  • Regina Daniels ta bayyanawa yan Najeriya cewa ita ba ta amfani da kayan mata kuma ba zata taba amfani da su ba

Yan Najeriya sun waye gari cikin musayar yawun dake gudana tsakanin Regina Daniels matar Biloniya, Ned Nwoko, da mai kayan mata, Jaruma Empire.

Zaku tuna cewa Regina ta tuhumci Jaruma da amfani da sunanta wajen tallan 'kayanmata' duk da cewa lokacin da sukayi yarjejeniya ya wuce.

Jaruma kuwa tayi martani mai zafi inda ta bayyana cewa musamman ta biya Regina Daniel N10 million don yi mata talla.

Kara karanta wannan

Dama can ni Musulma ce kuma 'yar Saudiyya, kawai Sallah ne bana yi - BBNaija Gifty

A cewarta, Regina ta raina mata hankali saboda sau uku tayi mata talla cikin watanni shida sabanin yarjejeniyar da suka yi.

Tace:

"Cikin watanni 6, Regina ta yi posting Jaruma sau 3! Ko dan ta ga ina Dubai za ta iya abinda ta ga dama."

Jaruma ta lissafa hidiman da ta yiwa Regina

A jawabin da Jaruma ta saki a shafinta na Instagram, ya bayyana irin hidindimun da ta yiwa Regina Daniels da mukarrabanta.

Ta lissafa cewa:

1. Ta baiwa mahaifyarta N1m ranar murnar ranar haihuwa

2. Ta siyawa Regina headphone na N120k

3. Ta shirya mata liyafan kimanin N172k

4. Ta baiwa hadiman Regina N300k

5. Ta baiwa hadiman kishiyarta, Laila Nwoko, N400k

6. Ta sayawa mahaifiyar Regina leshin N500k

Kara karanta wannan

'Yan dadi Afrika: Yadda mata 3 suka bar kasashensu na turai suka kauro Afrika, Najeriya

Tace:

"Na sayawa mahaifiyarki leshin N500k. Mun yi liyafa a gidan Sammy, na yi likin N100k, a wajen shan giya kuma na yi likin 200k."

Zan fallasa bidiyonki

A cigaba da martanin, Jaruma ta bayyana cewa zata bayyana bidiyoyin da Regina na talla kamar yadda sukayi yarjejeniya.

"Zan daura komai yau saboda kada gobe ki ce Jaruma na amfani da ke wajen talla," Jaruma tace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng