Karancin albashi: Mun maida lamarinmu ga Ubangiji inji wasu Malamai da Ma’aikatan jihar Kogi

Karancin albashi: Mun maida lamarinmu ga Ubangiji inji wasu Malamai da Ma’aikatan jihar Kogi

  • A jihar Kogi malaman makarantun firamare da ma’aikatan kananan hukumomi suna shan wahala.
  • Wasu ma’aikata sun ce ana zaftare masu kudi a cikin albashinsu, game da halin tsadar rayuwa.
  • Amma Gwamna Yahaya Bello tace babu ma’aikaci da yake bin Gwamnatin jihar Kogi bashi a yau.

Kogi - Wasu malaman makarantun firamare da ma’aikatan kananan hukumomi a jihar Kogi sun koka cewa gwamnati tayi watsi da su, ba ta jin tausayinsu.

Jaridar Vanguard ta rahoto kananan ma’aikatan suna kokawa da gwamnatin Alhaji Yahaya Bello.

Sai dai gwamnatin jihar Kogi tace ta biya ma’aikata dukkanin albashinna su, amma wasu daga cikinsu sun ce ba a biyansu cikakken kudinsu a karsen wata.

Da ‘yan jarida suka yi hira da wasu ma’aikatan makarantan da kananan hukumomi, sun bayyana cewa rayuwa tayi masu matukar wahala a yanayin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Dakarun Hisbah sun damke karuwai 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

Ma’aikatan sun ce gwamnatin Yahaya Bello ta kawo wasu sababbin tsare-tsaren biyan albashi, suka ce tun daga nan ake zaftare masu kudi a kowane wata.

Daga N45, 000, na koma karbar N16, 000

Wata daga cikin ma’aikatan da ta zanta da Vanguard a wayar salula tace abin da ake biyanta da shi ne N45, 000, amma yanzu albashin na ta ya koma N16, 000.

Gwamnan jihar Kogi
Yahaya Bello na son zama Shugaban kasa Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

“Abin da na karba karshe shi ne N16, 000. Ya kamata ace ana biya na N45, 000 a matsayin wanda take mataki na 7 a wajen aiki.” – Wata ma’aikaciya.

Wata malama da ta zanta da manema labaran a boye tace za ta fara kasuwanci domin ana samun gibi yanzu a albashinta, tace ta nemi bashi amma an hana ta.

Kara karanta wannan

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

Akwai wani tsohon ma’aikaci da yayi ritaya yace 40% kacal maidakinsa take samu a albashinta. Duk da haka kuma yace ba a biya ta albashinta na Satumba ba.

Binciken da jaridar tayi ya nuna cewa ma’aikatan kananan hukumomi ne wannan sabon tsari da aka kawo ya shafa, ana cire wani kaso daga cikin kudin na su.

Da aka yi hira da gwamna, yace ya biya kowa albashi, yace jihar ba za ta zaunu idan da bashi a kansa ba.

Badakala a ma'aikatar sufuri?

A makon jiya aka ji Gwamnatin Najeriya ta dawo da tsarin da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya soke shekaru 10 da suka wuce saboda kwadayin kudin shiga.

Ministan sufuri na tarayya, Rotimi Amaechi ake zargi ya shiga ya fita, har aka bada kwangilar kula da ruwan Najeriya ga wasu kamfanonin da ba su san aiki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng