Sojojin sama sun gano mabuyar ‘Yan bindiga a kauyukan Kaduna, sun buda masu wuta

Sojojin sama sun gano mabuyar ‘Yan bindiga a kauyukan Kaduna, sun buda masu wuta

‘Yan bindiga da-dama ake zargin sun mutu a wani hari da aka kai masu da jiragen sama a Kaduna.

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da wannan kokari da dakarun sojojin Najeriya suka yi dazu.

A jawabin da aka fitar, Gwamna Nasir El-Rufai ya yabawa sojojin kasar, ya kuma bukaci su kara kokari.

Kaduna - Jami’an tsaron Najeriya sun sake samun galaba a kan wasu ‘yan bindiga a wasu hare-hare da suka kai a kewayen karamar hukumar Chikun.

Inside Kaduna ta fitar da rahoto inda ta bayyana nasarar da sojojin suka samu a kan ‘yan bindigan.

Jaridar ba ta iya bayyana adadin ‘yan bindigan da aka kashe daga luguden wutan da aka yi ba, amma an tabbatar da cewa an hallaka miyagu da-dama.

Majiya daga gidan soja ta tabbatar da cewa an yi wa ‘yan bindiga rugu-rugu a kauyukan Kauwuri da Gaude, inda ake zargin bata-garin suna fakewa a nan.

Kara karanta wannan

‘Yan Boko Haram sun sace matafiya, sun dawo da Musulmai, sun yi gaba da sauran fasinjoji

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Binciken da jami’an tsaron suka yi da kuma bayanan sirri sun tabbatar akwai ‘yan bindiga da-dama da suke samun mafaka a yankin wadannan kauyuka.

An yi lugude a Kauwuri da Gaude

Rahoton yace a harin farko, jirgin yakin sojoji ya tarwatsa gungun ‘yan bindiga a garin Kauwuri. Sojoji sun hangi wasu ‘yan bindigan na tserewa daga yankin.

El-Rufai
Shugaban hafsun soji da Gwamnan Kaduna Hoto: Samuel Aruwan
Asali: Facebook

Bayan nan sai aka tura wasu dakaru dauke manyan makamai a jirgin sama mai saukar ungulu, ya sauka kasa daf da jama’a domin tarwatsa ‘yan bindigan.

An kai hari na biyun a Gaude bayan sojoji sun gano inda ‘yan bindigan suke boyewa. A nan ma an hangi miyagun suna neman boyewa a karkashin bishiyoyi.

Samuel Aruwan ya fitar da jawabi

Kamar yadda kwamishinan harkokin cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya bada sanarwa, daga nan ne sai aka yi wa wadannan miyagu luguden wuta.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da masu samar da kayan shaye-shaye da barasar bogi mai cutarwa

Gwamna Nasir El-Rufai ya ji dadin abin da ya faru, ya kuma yabawa jami’an tsaro. A karshe ya bukaci sojojin su dage, tare da kira ga mutane su sa sa idanu.

Harin da Boko Haram suka kai a Borno

Wasu sojojin Boko Haram na bangaren dakarun ISWAP sun tare mutane a hanyar Borno jiya, inda aka ji sun bukaci wadanda aka kama su karanta Al-Kur’ani.

Wani dattijo da ya tsallake rijiya da baya, ya bada labarin abin da ya gani. Wannan Bawan Allah yace an kyale shi ne bayan an ga yana fama da ciwon sukari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng