Sunayen Sultan 19 da aka yi bayan Mujaddadi Shehu Danfodio da shekarun da suka yi mulki
A shekarar nan ne Mai alfarma Sa’ad Abubakar III yake ciki shekara 15 da zama Sarkin Musulmi.
Mun tattaro jerin duka wadanda suka gaji rawanin Mujaddadi Shehu Usman Danfodio a tarihin Najeriya.
Bayan Shehu Danfodio ya kafa daula a shekarar 1804, an samu ‘ya ‘ya da jikokinsa 19 da suka hau mulki.
Bayan jihadin Mujaddadi Shehu Usman Danfodio ne aka kafa daular Musulunci a Najeriya. Wadanda suka zo bayan Shehu sun karbi sarautar Sarkin Musulmai.
Yayin da Mai alfarma Sarkin Musulmi mai-ci, Muhammad Sa’ad Abubakar III yake cika shekaru 15 a mulki, mun kawo ragowar Amir al-Mu´minin (Sultan) da aka yi.
Daga shekarar 1817 zuwa 2021, an yi Sarakunan Musulmai 19 a Najeriya. An fara ne daga Muhammadu Bello, babban ‘dan Shehu Usman Danfodio a Duniya.
Bayan rasuwar Bello, sai ‘danuwansa, Abubakar Atiku ya karbi mulki. Daga baya ‘ya ‘yan Bello sun yi rike daula; Ali ‘Dan Bello, Amadu Atiku, Ali Karami da dai sauransu.

Kara karanta wannan
Mufti Menk ya gabatar da Lakca a taron murnar cikar Sarkin Musulmi shekaru 15 kan mulki
Ahmadu Rufai shi ne ‘dan cikin Usman Danfodio na karshe da ya yi mulki a Daular Usmaniyya.

Asali: Facebook
An tunbuke Sultan Ibrahim Dasuki a 1996
Ibrahim Dasuki ne kadai Sarkin Musulmin da aka sauke daga kan karagar mulki a tarihi. Bayan an tubuke Sultan Dasuki, sai aka nada ‘danuwansa, Muhammad Maccido.
Da Sultan ya rasu a shekarar 2006, Sa’ad Abubakar III ya karbi ragama. A cikin Sarakunan da aka yi, Sadiq III ne wanda ya fi kowa dadewa, ya shafe shekaru har 50 a mulki.
Ga cikakken jerin nan kamar yadda yake a shafin Wikipedia
Sarakunan Musulmi da shekarun da suka yi mulki
1. Muhammadu Bello (1817 – 1837)
2. Abubakar Atiku (1837 – 1842)
3. Ali babba ‘Dan Bello (1842 – 1859)
4. Ahmadu Atiku (1859 – 1866)

Kara karanta wannan
Shehu Idris, Ado Bayero, Lamido da Sarakunan Arewa da suka yi tsawon rai a karagar mulki
5. Ali Karami (1866 – 1867)
6. Ahmadu Rufai (1867 – 1873)
7. Abubakar Atiku II (1873 – 1877)
8. Muazu (1887 – 1881)
9. Umaru Ali (1881 – 1991)
10. Abdurrahman Abubakar (1891 – 1902)
Ragowar Sarakunan musulman su ne:
11. Muhammadu Attahiru (1902 – 1903)
12. Muhammadu Attahiru II (1903 – 1915)
13. Muhammadu Ahmadu (1915 – 1924)
14. Muhammadu ‘Dan Muhammadu (1924 – 1931)
15. Hassan ‘Dan Muazu Ahmadu (1931 – 1938)
16. Sadiq Abubakar III (1938 – 1988)
17. Ibrahim Dasuki (1988 – 1996)
18. Muhammadu Maccido (1996 – 2006)
19. Muhammadu Sa’ad Abubakar III (2006 – yau)
Sarkin Musulmi ya shekara 15 a karaga
Dazu kun ji cewa an gayyato Shehin malamin Duniya, Mufti Ismail Menk ya gabatar da lacca ta musamman yayin da Sarkin Musulmi ya cika shekaru 15 kan mulki.
Mufti Menk yayi jawabi a kan muhimmancin zaman lafiya da kuma yadda mutanen Arewa suka dauki addini da muhimmanci, yana yabon rikon addinin 'Yan Arewa.
Asali: Legit.ng