Mahaifiyar Sheƙau: Ya jefa ni cikin ƙunci, ni da shi Shari'a sai a lahira
- Mahaifiyar tsohon shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ta yi magana game da danta
- Fatima Abubakar ta ce bata da masaniya kan cewa ko Shekau yana da 'ya'ya ko kuma ba shi da su
- Kazalika, ta ce babu wani abu da zai hada da shi ko ya mutu ko yana raye illa shari'a da Allah zai musu don kunci da ya jefa ta
Fatima Abubakar, mahaifiyar tsohon shugaban kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, Abubakar Shekau, ta ce bata da masaniya ko danta yana da yara.
Fatima, wacce ta bayana hakan a wani hira da ta yi da Trust TV, ta ce ko yana raye ko mace, babu wani abu da ke tsakaninta da shi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Fatima ta bayyana cewa Shekau ya jefa ta cikin ukuba har ta kai cewa ta cire rai da shi.
Ta ce:
"A bangare na, ni na tsuguna na haifi shi, wannan shine abin da kadai ke tsakanin mu. Ko yana da rai ko ya mutu; mun raba jiha.
"Ban taba sanin ko yana da 'ya'ya ba ko kuma ba shi da su. Ya jefa ni cikin bakin ciki. Allah zai yi hisabi tsakanin mu a ranar gobe kiyama."
A watan Mayun shekarar 2021, an kashe Shekau yayin fada tsakaninsa da mayakin kungiyar Islamic State in West Africa Province (ISWAP).
Rahotanni sun ce ya halaka kansa a yayin da ya lura mayakan na ISWAP na daf da cin masa da ransa.
Dakarun sojojin Nigeria sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram 38 cikin makonni 2, DHQ
A wani rahoton, hedkwatar tsaro ta ce rundunar Operation Hadin Kai ta sojojin Nigeria ta samu nasarar halaka a kalla ‘yan Boko Haram 38 a cikin makonni 2 cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na Facebook.
Bernard Onyeuko, mukaddashin darektan watsa labaran soji ya sanar da hakan yayin bayar da bayani akan ayyukan da sojoji su ka aiwatar tsakanin ranar 14 ga watan Oktoba zuwa 28 ga watan.
Onyeuko ya ce an kama ‘yan ta’adda 11 tare da masu kai mu su labarai da kuma masu kai mu su bayanan sirri har da ma su kai mu su kayan masarufi kamar yadda ya zo cikin sanarwar.
Asali: Legit.ng