Kamen Obi Cubana: 'Dan DG na DSS ya caccaki EFCC, ya ce "karnukan 'yan siyasa" ne
- 'Dan darakta janar na DSS, Abba Yusuf Bichi, ya kira Obi Cubana da mutum mai mutunci da daraja
- A yayin martanin wani tsokaci a wallafar, ya kwatanta EFCC da karnukan 'yan siyasa a kasar nan
- A ranar Litinin EFCC ta damke Cubana inda ta ke zarginsa da halasta kudin haram da zambar haraji
Abba Bichi, dan darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ya caccaki kamen fitaccen biloniyan Najeriya da hukumar EFCC ta yi mai suna Obinna Iyiegbu wanda aka fi sani da Obi Cubana.
A ranar Litinin, hukumar yaki da rashawa ta damke Obi Cubana kan zargin halasta kudin haram da zambar haraji.
Sai dai, Abba Yusuf Bichi wanda dan kwallo ne, ya wallafa hoton Obi Cubana inda ya rubuta : "Mutum mai girma da mutunci" a shafinsa na Instagram.
A yayin da wani mai tsokaci ya janyo hankalinsa kan zargi ne kuma ya bari a bincika domin gano gaskiya, Abba ya yi martani inda ya ce EFCC ta na yi wa 'yan siyasa aiki ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Su karnukan 'yan siyasa ne, shiyasa! Ina mamakin yadda mutum mai hankali zai zabi dan siyasa kan mutum mai aiki tukuru! Shiyasa Najeriya duk ta lalace," Abba ya yi martani.
A cikin sa'o'i 12 da wallafar ta yi, ta janyo tsokaci sama da dari.
Obi Cubana ya shiga kanun labarai a watan Yuli yayin da ya hada wa mahaifiyarsa gagarumin bikin mutuwar ta a Oba, jihar Anambra, inda manyan masu kumbar susa a Najeriya suka samu halarta.
Har a halin yanzu, hukumar yaki da rashawan ba ta ce komai kan kamensa ba.
Dalla-dalla: Dalilai 2 da suka sa EFCC ta yi ram da biloniya Obi Cubana
A wani labari na daban, ba sabon labari ba ne cewa Obinna Iyiegbu, wanda aka fi sani da Obi Cubana ya na hannun hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC a Abuja.
Legit.ng ta tattaro muku cewa, hukumar yaki da rashawan ta gayyacesa ne kan dalilai guda biyu kwarara.
Domin bayani ga makaranta, Legit.ng ta bayyana dalilai biyu da yasa Obi Cubana ya ke hannun EFCC domin amsa tambayoyi.
Asali: Legit.ng