KAI TSAYE: Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP

KAI TSAYE: Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP

Bayan yunkurin hana taron gangamin da tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Uche Secondus, yayi a kotu, akalla wakilai 3600 sun taru a farfajiyar Eagle Square.

Hakan ya biyo bayan watsi da karar Uche Secondus ranar Juma'a a kotun daukaka kara.

Wannan taro zai gudana tsakanin ranar Asabar, 30 ga Oktoba da Lahadi, 31.

A wannan taro, za'a zabi sabbin shugabannin jam'iyyar da zasu ja ragamar lamura a nan gaba.

Kimanin kujeru 21 za'a dabe kuma an tantance mutane 27 da zasuyi takaran wadannan kujeru, kamar yadda Legit ta tattaro muku.

Shugaban wannan taron gangami wanda shine gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana cewa kujeru uku kadai ya rage ba'ayi ittifaki kuma aka yarje wadanda zasu haye ba.

Kujerun sune na mataimakin jam'iyyar (na Kudu), shugaban matasa da Odito Janar.

Zamu kawo muku rahotanni kai tsaye idan aka fara taron.

Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Iyorchia Ayu, ya zama sabon Shugaban uwar jam'iyyar PDP.

Ayu, wanda bai samu wanda yayi takara da shi ba zai jagoranci jam'iyyar da sauran shugabanni 20 da aka zaba.

KAI TSAYE: Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP
KAI TSAYE: Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP
Asali: UGC

Deligata na jihar Kano, Jigawa, Kwara da Legas sun kada kuri'unsu

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya jagoranci yan jam'iyyar PDP na jihar Kano wajen kada kuri'unsu a taron gangamin dake gudana.

Mabiya madugun siyasan na ta ihun 'Kwankwaso' Kwankwaso'

Hakazalika tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya jagoranci al'mmar jihar wajen kada kuri'unsu.

Mutane Kwara da Legas kuwa yanzu haka na kada kuri'unsu.

An yi kira ga jihar Nasarawa da Neja su shirya.

Mai sanarwan yace mutum 58 zasu kada kuri'a cikin yan jihar Nasarawa yayinda mutum 76 zasu yi daga Neja

Rahoton Premium Times

Jigogin PDP sun caccaki gwamnatin Buhari

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umari Fintiri, a jawabin da yayi a taron ya bayyana cewa abubuwa basu taba muni a Najeriya ba kamar yadda sukayi a gwamnatin APC.

Yace lallai akwai bukatar jam'iyyar PDP ta koma kan ragamar mulki.

Hakazalika shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan tarayya, Enyinnanya Abaribe, a jawabinsa yace:

"Mutane sun kosa wannan kashe-kashe da sace-sacen kudin baitul mali da APC ke yi. Jahilar gwamnati da ta gaza komai yayinda yan bindiga suka mamaye titunanmu."

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kada kuri'arsa

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya kada kuri'arsa a zaben sabbin shugabannin PDP dake gudana.

Atiku wanda ke tare da jagoran darikar Kwankwasiyya a taron ya samu rakiyar masoya da mabiyansa.

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

An kaddamar da taron gangamin na bana

Misalin karfe 1:05 na rana, an bude taron gangamin da wakan Najeriya.

Sannan Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Kano, Shehu Wada ya yi addu'an bude taro na Musulmai, kuma gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, yayi na Kirista.

Wakilan jihohin Najeriya 3600 sun halarta illa na jihar Ogun da Ondo, da wasu wasu jihohin yankin Yarbawa inda aka samu matsala makonnin da suka gabata wajen zabensu.

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
Asali: UGC

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
Asali: UGC

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
Asali: UGC

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
Asali: UGC

Online view pixel