KAI TSAYE: Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP

All posts
Key Events
Analysis
Exclusive
5 Posts
Sort by
Our live updates have concluded for the day. Catch up on everything you missed below.
Mudathir Ishaq avatar Abdul Rahman Rashid avatar
daga Mudathir Ishaq and Abdul Rahman Rashid

Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Iyorchia Ayu, ya zama sabon Shugaban uwar jam'iyyar PDP.

Ayu, wanda bai samu wanda yayi takara da shi ba zai jagoranci jam'iyyar da sauran shugabanni 20 da aka zaba.

KAI TSAYE: Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP
KAI TSAYE: Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP
Source: UGC

Mudathir Ishaq avatar Abdul Rahman Rashid avatar
daga Mudathir Ishaq and Abdul Rahman Rashid

Deligata na jihar Kano, Jigawa, Kwara da Legas sun kada kuri'unsu

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya jagoranci yan jam'iyyar PDP na jihar Kano wajen kada kuri'unsu a taron gangamin dake gudana.

Mabiya madugun siyasan na ta ihun 'Kwankwaso' Kwankwaso'

Hakazalika tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya jagoranci al'mmar jihar wajen kada kuri'unsu.

Mutane Kwara da Legas kuwa yanzu haka na kada kuri'unsu.

An yi kira ga jihar Nasarawa da Neja su shirya.

Mai sanarwan yace mutum 58 zasu kada kuri'a cikin yan jihar Nasarawa yayinda mutum 76 zasu yi daga Neja

Rahoton Premium Times

Mudathir Ishaq avatar Abdul Rahman Rashid avatar
daga Mudathir Ishaq and Abdul Rahman Rashid

Jigogin PDP sun caccaki gwamnatin Buhari

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umari Fintiri, a jawabin da yayi a taron ya bayyana cewa abubuwa basu taba muni a Najeriya ba kamar yadda sukayi a gwamnatin APC.

Yace lallai akwai bukatar jam'iyyar PDP ta koma kan ragamar mulki.

Hakazalika shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan tarayya, Enyinnanya Abaribe, a jawabinsa yace:

"Mutane sun kosa wannan kashe-kashe da sace-sacen kudin baitul mali da APC ke yi. Jahilar gwamnati da ta gaza komai yayinda yan bindiga suka mamaye titunanmu."

Mudathir Ishaq avatar Abdul Rahman Rashid avatar
daga Mudathir Ishaq and Abdul Rahman Rashid

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kada kuri'arsa

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya kada kuri'arsa a zaben sabbin shugabannin PDP dake gudana.

Atiku wanda ke tare da jagoran darikar Kwankwasiyya a taron ya samu rakiyar masoya da mabiyansa.

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja
KAI TSAYE: Yadda taron gangamin jam'iyyar PDP ke gudana a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Mudathir Ishaq avatar Abdul Rahman Rashid avatar
daga Mudathir Ishaq and Abdul Rahman Rashid

An kaddamar da taron gangamin na bana

Misalin karfe 1:05 na rana, an bude taron gangamin da wakan Najeriya.

Sannan Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Kano, Shehu Wada ya yi addu'an bude taro na Musulmai, kuma gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, yayi na Kirista.

Wakilan jihohin Najeriya 3600 sun halarta illa na jihar Ogun da Ondo, da wasu wasu jihohin yankin Yarbawa inda aka samu matsala makonnin da suka gabata wajen zabensu.