Da duminsa: Jami'an tsaro sun dira gidan alkalin kotun koli a Abuja

Da duminsa: Jami'an tsaro sun dira gidan alkalin kotun koli a Abuja

  • Jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda sun dira gidan alkalin kotun koli, Mary Odili, da ke Abuja
  • Mary Odili ita ce matar tsohon gwamnan jihar Ribas, Peter Odili, wanda hukumar EFCC ke yi wa kwanton bauna
  • Alkali Mary Odili wacce ita ce ta biyu a matsayi a kotun kolin Najeriya, har yanzu ba a san dalilin zuwan jami'an tsaron gidan ta ba

FCT, Abuja - Jami'an tsaro a ranar Juma'a sun dira gidan Mary Odili, alkali a kotun koli da ke Abuja.

Alkalin kotun kolin mata ce ga Peter Odili, tsohon gwamnan jihar Ribas wanda a halin yanzu ya ke cikin wadanda hukumar yaki da rashawa ta kasa, EFCC suka sanya wa ido.

Kamar yadda TheCable ta wallafa, Har yanzu dai babu cikakken bayani kan abinda ke faruwa a gidan.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An tsinci gawar jami'in kwastam da miyagu suka yi garkuwa da shi

Da duminsa: Jami'an tsaro sun dira gidan alkalin kotun koli, Mary Odili, a Abuja
Da duminsa: Jami'an tsaro sun dira gidan alkalin kotun koli, Mary Odili, a Abuja
Asali: Original

Kamar yadda wata majiya ta ce, jami'an tsaron da suka tsinkayi gidan sun hada da jami'an 'yan sanda da na sojojin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har a yayin rubuta wannan rahoton, ba a san dalilin da yasa jami'an tsaron suka shiga gidan alkalin ba, TheCable ta wallafa.

Alkalin wacce a halin yanzu ita ce mafi daraja ta biyu a alkalan kotun kolin, ana tsammanin za ta kasance cikin alkalai bakwai da za su sanar da matsayar karshe kan rikicin harajin da ya shafi jihohi da gwamnatin tarayya.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: