Kasafin 2022: Ta kacame tsakanin sanatoci kan raba wa mazabu ayyukan tituna

Kasafin 2022: Ta kacame tsakanin sanatoci kan raba wa mazabu ayyukan tituna

  • Hayaniya ta kacame tsakanin sanatoci a majalisar dattawa kan yadda aka rabe ayyukan titunan kasar nan a kasafin shekara mai zuwa
  • Sanata Sekibo daga jihar Ribas ya tuhumi Fashola da zabga aikin titi mai tsayin 1,400Km a arewa yayin da aka ware 89.9 na kudu
  • Sanata Aliero ya kare hakan inda ya ce yanayin kudin da tituna ke ci a arewa babu yawa, amma sai Sekibo ya harzuka tare da cewa ya na kare Fashola

FCT, Abuja - A ranar Juma'a sanatoci sun yi arangama kan rarrabe ayyukan tituna a kasafin kudin shekarar 2022.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawan domin kare kasafin kudin ma'aikatarsa wanda ya kai biliyan N450.

Fashola ya sanar da 'yan majalisar cewa an ware N350 biliyan domin yin tituna a fadin kasar nan, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

Kasafin 2022: Ta kacame tsakanin sanatoci kan raba wa mazabu ayyukan tituna
Kasafin 2022: Ta kacame tsakanin sanatoci kan raba wa mazabu ayyukan tituna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Rikicin ya fara ne yayin da Sanata George Sekibo daga jihar Ribas ya bayyana cewa za a gyara titi mai tsayin kilomita 1,400 a yanki daya a arewa yayin da aka bar kudu kudu da titi mai tsayin kilomita 89.9.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan ana duba yankuna, ya dace ne a kai daukin yadda ya dace yadda kowa zai zama cikin farin ciki," dan majalisar ya sanar da Fashola.

Shugaban kwamitin, Adamu Aliero, ya katse tare da yin kira ga Sekibo da ya sani tare da duba irin kudin da kowanne aiki zai ci a kowanne yanki.

"Idan akwai kudi har biliyan dari shida da za a raba domin yin tituna a yankuna shida, kowanne yanki zai samu biliyan dari saboda adalci da daidaito.
"Sai dai kuma biliyan dari za a iya amfani da ita wurin yin titi mai tsayin kilomita dari biyu a arewa maso gabas amma ba za ta isa a yi titi mai tsayin kilomita talatin ba a kudu kudu saboda yanayin wuri," yace.

Kara karanta wannan

Sultan ya yi wa direban da ya mayar da N500,000 da aka manta a kekensa kyauta mai tsoka

Amma kuma, Sekibo sai ya katse sanata Adamu Aliero inda ya tuhume sa da mayar da martani a madadin ministan, Daily Trust ta wallafa.

"Ansa masa kake? ya tambaya Aliero wanda ya yi martani da cewa: "Ina dai fada maka abinda na sani ne wanda kuma na san ka san shi sosai."

Wani mamban kwamitin, Sanata Danladi Sankara daga jihar Jigawa, ya ce dukkan sassan kasar nan na koke kan tituna kuma ba zai yuwu dukkan kasar nan ta samu tituna ba saboda Najeriya ta na da girma.

Buhari ya kashe sama da N45bn domin inganta rayuwar Katsinawa, Masari

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce gwamnatin tarayya ta kashe sama da naira biliyan arba'iin da biyar kan shirye-shiryen tallafi daban-daban domin inganta rayuwar mutane a jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar da rukunin shaguna da gidan saukar baki na ma'aikatan lafiya a jihar Katsina wanda kungiyarsu ta gina.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Wani Mutumi ya damfari malamin addini miliyan N1.2m, An gurfanar da shi gaban Kotu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng