Funmilayo Ransome-Kuti: Abubuwa 4 game da macen da ta fara tuka mota a Najeriya
- Funmilayo Ransome-Kuti fitacciyar 'yar siyasa ce da ta zama mace ta farko da ta fara tuka mota a Najeriya
- Funmilayo ta cire sunan turancinta na Abigail bayan dawowa daga Birtaniya ganin banbancin launin fata da ake nunawa
- Sojoji sama da 1,000 ne suka yi sanadin mutuwar ta bayan jefo ta daga bene hawa biyu da suka yi har ta samu miyagun raunika
Funmilayo Ransome-Kuti ita ce mace ta farko da ta fara tuka mota a Najeriya amma ba ta nan kadai ta yi suna ba, akwai abubuwa masu yawa game da jarumar.
Tabbas macen mai kamar maza ta kasance malama kuma 'yar siyasa wacce ta ke gaba-gaba wurin rajin kare hakkin mata a kasar nan kafin mutuwar ta.
Legit.ng ta tattaro wasu muhimman abubuwa hudu da ya dace mai karatu ya sani game da jajirtacciyar mai kare hakkin matan.
1. Funmilayo ita ce mahaifiyar fitaccen mawakin Afrika, Fela Kuti kuma ta na da alakar jini da Wole Soyinka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Babu shakka tsatson Funmilayo ya haifar da wasu muhimman mutane da suka taba rayuwa a Najeriya, wasu kuma har yanzu suna raye.
2. Ta bar sunan ta na Kiristanci
Funmilayo ta cire Frances Abigail daga sunanta da aka san ta. Ta yi hakan ne bayan ta dawo daga Birtaniya inda ta yi karatu.
Wannan ya biyo bayan banbancin launin fata da ta gani a yayin zaman ta da Birtaniya.
3. Ita ce mace ta farko da aka bai wa mukami a Western House
Baya ga samun sarautar Oloye ta kasar Yarabawa, Funmilayo ita ce mace ta farko da aka taba bai wa mukami a Western House.
Western House majalisa ce da aka kafa bayan mulkin mallaka kuma ana kallon ta ne a majalisar kasa ko ta gwamnatin yanki wacce ke da murya tare da tsayawa mutane a gaban turawan mulkin mallaka.
A yayin rayuwar ta, mai rajin kare hakkin matan ta samu lambobin yabo tare da karramawa daban-daban.
4. Yadda ta rasu
Bayan raunika da ta samu a samamen da sojoji suka kai gidan ta, Funmilayo ta rasu ta na da shekaru 77 a ranar 13 ga watan Afirulun 1978.
Kamar yadda aka gano, sojoji sama da 1,000 sun zagaye gidan ta kuma sun shiga da karfi da yaji inda suka dinga cin zarafin mutanen gidan.
Bayan barnar da suka yi a gidan, sun wurgo Funmilayo daga bene hawa na biyu, wanda hakan yasa ta samu raunika har ta kwanta asibiti wanda daga bisani ta rasu.
Asali: Legit.ng