Jami’o’i da manyan makarantu 30 da Shugaba Buhari ya kirkira daga 2015 zuwa 2021

Jami’o’i da manyan makarantu 30 da Shugaba Buhari ya kirkira daga 2015 zuwa 2021

  • Muhammadu Buhari ya kirkiri sababbin jami’o’i da manyan makarantun sakandare 30 a Najeriya.
  • Gwamnatin Tarayya ta kafa wasu makarantu, yayin da aka karawa wasunsu girma a jihohin kasar nan.
  • Ana ta kirkirar sababbin makarantun ne a lokacin da ake kukan ba a kula da wadanda ake da su a kasa.

Nigeria - Wani bincike na musamman da Daily Trust ta yi ya nuna yadda gwamnatin tarayya ta ke kafa sababbin manyan makarantu a jihohin Najeriya.

Tsakanin shekarar 2015 da 2021, gwamnatin Muhammadu Buhari ta kirkiro manyan makarantu na gaba da sakandare akalla 30, duk da ana kukan rashin kudi.

Rahoton da aka fitar ya nuna an kirkiro sababbin jami’o’in gwamnati 11, da kwalejin horas da malamai 9, da kuma manyan makarantun koyar da aiki 10.

Kara karanta wannan

An daure makiyayi daurin rai da rai bisa laifin gwada kashe wani da mallakar mugun makami

A shekarar nan gwamnatin tarayya ta fitar da Naira biliyan 18 domin a fara aikin gina wasu jami’o’i na musamman da Buhari ya amince a kafa a kasar.

An kirkiri jami’ar sojoji a jihar Borno da ta sufuri a garin Daura da ke Katsina, da wata jami’ar koyan aikin gona a Zuru, da ta kiwon lafiya a jihar Benuwai.

Akwai kwalejin horas da malamai a Jama'are, Isu, Kirikasamma da Ekidolor. Sannan an kirkiri makarantun koyon aiki a Osun, Gombe, Borno da sauransu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan majalisar tarayya suna taimakawa sosai wajen kafa makarantun gaba da sakandare a Najeriya.

Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Su wanene sababbin jami’o’in tarayya da aka kafa:

Jami’o’i da aka kikiro sune Nigerian Maritime University, Okerenkoko (2018); Air Force Institute of Technology, Kaduna (2018); Nigerian Army University, Biu (2018; Federal University of Transportation, Daura, Katsina State (2018); Federal University of Agriculture, Zuru, Kebbi State (2020) da University of Health Technology, Otukpo Benue State (2020).

Kara karanta wannan

Rigimar Shekarau da sauran masu fada da Gwamnoni ta kara jagwalgwalewa a APC

Ragowar sune; Federal University of Technology, Babura, Jigawa State (2021); Federal University of Technology, Ikot Abasi, Akwa Ibom State (2021); Federal University of Health Sciences, Azare, Bauchi State (2021); Nigeria Air Force University, Kaduna (2018) and the Federal University of Health Sciences, Ila Orangun, Osun State (2021).

An kawo sababbin polytechnic

Binciken ya kuma nuna akwai makarantun koyon aiki na tarayya watau polytechnics 10:

Federal Polytechnic Ile-Oluji, Ondo State; Federal Polytechnic, Daura, Katsina State; Federal Polytechnic Kaltungo, Gombe State; Federal Polytechnic Ayede, Oyo State; Federal Polytechnic Munguno, Borno State;

Sai Federal Polytechnic N’yak, Shendam, Plateau State; Federal Polytechnic Ohodo, Enugu State; Federal Polytechnic Ugep, Cross Rivers State; Federal Polytechnic Wannune, Benue State and the Federal Polytechnic, Orogun, Delta state.

Kwalejin horas da malamai da aka kafa

An samu sababbin makarantu na koyar da malamai a wasu jihohi a ‘yan shekarun nan:

Federal College of Education, Iwo; Federal college of Education, Odugbo; Federal College of Education, Isu; Federal College of Education, Ekiadolor; Federal College of Education, Gidan Madi; Federal College of Education, Jama’are; Federal College of Education, Birnin Kudu and Federal College of Agriculture, Kirikasamma.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

Fatara a Afghanistan

A kasar waje, an ji yadda mummunar fatara ta sa dole wasu iyaye su ke saida yaransu domin a samu abincin da za a ci, watanni kadan bayan Taliban ta karbi iko.

Akwai wanda ta bada ‘yar ta domin a yafe mata bashin N220, 000 da ta gaza biya. An samu iyayen da suka saida jaririyarsu a $200 domin su ciyar da sauran 'ya 'yansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng