Mijina ya yi barazanar kashe ni da 'ya'yana kuma ba abunda za'a yi, Mata ta nemi a datse igiyoyin aure a Kotu
- Wata mata ta garzaya kotu tana neman alkali ya shiga tsakaninta da mijinta saboda yana barzanar kashe ta da yayanta
- Matar tace mijin nata ba shi da imani, da zaran sun samu yar matsala ƙarama, sai ya kama jibgarta
- A nashi ɓangaren magidancin ya musanta dukkam ikirarin matar, kuma yace shi har yanzun yana ƙaunar matarsa
Abuja - Wata ma'aikaciyar gwamnati, Blessed Nwa, ta roƙi kotu a Abuja ranar Alhamis, ta datse igiyoyin aurenta da yakai na tsawon shekara biyu.
Vanguard ta rahoto cewa matar ta nemi a raba ta da mijinta, Ahamefula saboda barazanar da ya mata cewa zai kashe ta ya kashe ƴaƴanta.
A ƙarar da ta shigar, Nwa tace:
"Mijina ya mun barazanar kashe ni ya kashe yayan mu kuma ba abinda za'a masa. Na kai rahoto ga yan sanda, na kuma kai rahoto hukumar yaƙi da safarar mutane (NAPTIP)."
Dan Sarki a Arewa ya shiga jam'iyyar adawa, ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023
Shin ya halin mijin nata yake?
Matar ta bayyana wa kotun cewa mijinta ba shi da saukin sha'ani, kuma baya tausaya mata, da zaran sun samu saɓani sai ya lakaɗa mata dukan tsiya.
Hakanan kuma tace mijin nata ya mata barazanar sace ƴaƴan da suƙa haifa, kuma ba zata sake ganin su ba har abada.
Daga nan ta roki kotun ta datse igiyoyin aurensu sannan ta bada umarnin hana mijin ya sace mata ƴaƴa zuwa wani wuri da bata sani ba.
Shin mijin ya amsa laifukan da matar ke zarginsa?
A nashi ɓangare, wanda ake ƙara, Ahamefula, ya musanta duk zargin da matarsa ta ɗora a kansa, ya kuma roki kotun kada ta raba auren su.
A cewar magidancin, har yanzun yana ƙaunar matarsa kuma ba ya son ta gudu ta bar shi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Alƙalin kotun, mai shari'a Labaran Gusau, ya shawarci ma'auratan da su yi kokarin sasanta kan su a waje kafin kotu ta yanke hukunci.
Daga nan sai alkalin ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa 1 ga watan Disamba, lokacin da yake fatan zasu zo da rahoton sasancin da suka yi.
A wani labarin kuma Sheikh Abduljabbar ya sake caccakar Laiyoyinsa a Kotu, ya nemi a bashi dama ya kare kansa
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya sake neman a bashi dama ya kare kansa saboda ya fahimci Lauyiyinsa ba zasu iya ba.
A cewar shehin Malamin Lauyoyin na shi ba su da cikakkiyar kwarewa a ilimin addini, an yi taƙaddama a zaman kotun.
Asali: Legit.ng