Daliban sakandire sun sa an lakaɗawa malamai dukan kawo wuka, Gwamnati tace ba zata saɓu ba

Daliban sakandire sun sa an lakaɗawa malamai dukan kawo wuka, Gwamnati tace ba zata saɓu ba

  • Dalibai a jihar Ogun sun sa yan daba sun laƙadawa malaman su dukan tsiya har cikin makaranta
  • Gwamnatin jihar tace ba zata zuba ido tana kallon wannan rashin ɗa'a ba, kuma za'a kori duk wani ɗalibi da aka gano yana da hannu
  • Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha, Abayomi Arigbabu, yace tuni gwamnati ta fara ɗaukar matakan doka kan masu aikata haka

Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta yi barazanar korar duk wani ɗalibi mara ɗa'a biyo bayan rahotannin dukan malamai da ake ƙara samu a faɗin jihar.

Dailytrust ta rahoto cewa ɗalibai a jihar Ondo na lakaɗawa malamansu duka ko kuma su ɗebo yan daba su zane malaman nasu a wasu makarantu.

A ranar Litinin ɗinnan, wasu yan daba da ɗalibai suka ɗebo suka farmaki malamai a makarantar sakandiren Community High dake Ijoun ƙaramar hukumar Yewa North.

Kara karanta wannan

Bayan harin masallaci, Yan Banga sun hallaka Hakimi da ɗan uwansa a jihar Neja

Jihar Ogun
Daliban sakandire sun sa an lakaɗawa malamai dukan kawo wuka, Gwamnati tace ba zata saɓu ba Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla malamai biyu ne suka ji raunuka yayin harin yan daban da suka laƙada musu duka, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin wannan shine na farko?

Lamarin ya faru ne mako ɗaya bayan wani ɗalibi a makarantar Unity Hight dake wannan ƙaramar hukumar ya debo hayar yan daba sun zane malamai.

Hakanan kuma ranar Talata, wasu ɗalibai sun lakaɗawa malaminsu duka a makarantar Comprehensive High dake Ewekoro.

Malamin mai koyar da darasin lissafi ya sha duka ne bayan ya umarci wani ɗalibi ya daina dukan wata yarinya a lokacin da yake darasi.

Yadda Lamarin ya faru

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa malamin na tsaka da koyar da SS1 lokacin da ɗalibin ya shigo kai tsaye ya fara bugun yarinyar.

Mutumin yace:

"Malamin ya umarci yaron ya dakatar da bugun yarinyar, nan take sai ɗalibin ya koma kan malamin, ya dinga naushinsa ba sassautawa."

Kara karanta wannan

Fusatattun jam'an gari sun sheƙe wani ɗan leken asirin yan bindiga da iyalansa a Kaduna

Wane mataki gwamnati zata ɗauka?

Da yake martani kan yawaitar lamarin, kwamishinan Ilimi, kimiyya da fasaha, Farfesa Abayomi Arigbabu, yace za'a sallami ɗaliban sanan doka za tayi aiki akansu da kuma masu taimaka musu.

Yace gwamnati zata cigaba da yaƙi da irin wannan aikin kuma waɗan da aka cafke a baya an gurfanar da su gaban kotu.

A wani labarin kuma wani gwamnan APC yace lokaci ya yi da za'a kauce a baiwa mata wuri su jagoranci Najeriya

Gwamnan yace babu al'ummar da zata cigaba matukar ta yi watsi da mata domin mata jagorori ne nagari.

Yace tarihin Najeriya cike yake da jarumtar mata, kuma matukar ana son a cigaba sai an jawo su cikin harkar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: