Yanzu-yanzu: Abba Ruma, Ministan Noma a zamanin 'YarAdu'a ya rasu a Landan
- Allah ya yi wa tsohon ministan noma da ma’adanan ruwa, Dr Abba Sayyadi Ruma rasuwa
- Ya rasu ne a London inda ya je domin a duba lafiyar sa sakamakon ciwon suga da ya addabe shi
- Ya rasu ya na da shekaru 59 a duniya, ya kuma bar matan aure biyu da 'ya'ya 9 duk masu rai
Tsohon ministan noma da albarkatun ruwa, Dr Abba Sayyadi ruma ya riga mu gidan gaskiya.
Leadership ta rahoto cewa Ruma ya rasu ne a wani asibiti a birnin Landan.
Kawunsa kuma Danwairen Katsina, Alhaji Sada Salisu ya tabbatar da rasuwarsa tsohon ministan
A cewar Sada, marigayin ya yi fama da ciwon sukari na tsawon lokaci kafin rasuwarsa, rahoton Daily Trust.
Ya rasu ya na da shekaru 59 sannan ya bar mata 2 da yara 9.
Takaitacen Tarihin Ruma
An haife shi a ranar 13 ga watan Maris na 1962, marigayi Ruma minista ne wanda ya yi aiki tukuru a lokacin mulkin marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua.
Ruma ya rike kujerar shugaban hedkwatar kungiyar tattalin kudi don habaka harkar noma a Rome, kasar Italiya.
Tsohon ministan ya yi digirin sa na farko a bangaren tarihi a jami’ar Sokoto, ya yi digirin sa na biyu a harkokin kasashen waje daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria sannan ya yi digirin digirgir a jami’ar Abuja.
Allah ya yi wa jikar Ahmadu Bello Sardauna ta farko rasuwa
A wani rahoton, kun ji cewa jikar tsohon Firimiyan tsohuwar Yankin Arewacin Nigeria, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto ta riga mu gidan gaskiya.
Hajiya Hadiza ta rasu ne a Sokoto bayan fama da fajeruwar rashin lafiya kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.
An haife ta ne a shekarar 1960, shekarar da Najeriya ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.
Asali: Legit.ng