Buhari ya kashe sama da N45bn domin inganta rayuwar Katsinawa, Masari

Buhari ya kashe sama da N45bn domin inganta rayuwar Katsinawa, Masari

  • Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina ya ce gwamnatin Buhari ta kashe sama da N45bn domin inganta rayuwar jama'ar Katsina
  • Gwamnan ya ce gwamnatin Buhari ce ta farko da ta fara kai wa gidaje masu fama da matsanancin talauci tallafi a arewa
  • Masari ya sha alwashin biyan dukkan kudaden fansho da na garatuti da ake bin gwamnatin jihar Katsina kafin cikar wa'adin mulkinsa

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce gwamnatin tarayya ta kashe sama da naira biliyan arba'iin da biyar kan shirye-shiryen tallafi daban-daban domin inganta rayuwar mutane a jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar da rukunin shaguna da gidan saukar baki na ma'aikatan lafiya a jihar Katsina wanda kungiyarsu ta gina.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

Buhari ya kashe sama da N45bn domin inganta rayuwar Katsinawa, Masari
Buhari ya kashe sama da N45bn domin inganta rayuwar Katsinawa, Masari. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: Twitter

Ya ce shirye-shiryen tallafin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kirkiro sun taka rawar gani wurin kawo dauki da taimakon gidajen da ke fama da tsananin talauci a jihohin arewa.

"Kamar yadda al'adun mu suke a nan bangaren arewacin Najeriya, ka na tsufa, hidindimu suna cigaba da karuwa maka saboda ba mu da wani tsarin tallafi.
“A tsarin gidan gado ko kuma gidan yawa ne kadai ake samun tallafi kafin wannan na shugaban kasa Buhari ya zo.
"Wannan shi ne ginshikin tallafi inda kai tsaye ake bai wa marasa karfi taimako na a kalla dubu biyar kowanne wata.
“A irin wadannan shirye-shiryen kadai, daga watan Yulin shekarar nan, gwamnatin tarayya ta kashe sama da biliyan arba'in da biyar a jihar Katsina.
"Ina so ku kwatanta me kullen korona, rashin tsaro, faduwar farashin man fetur za su kasance," yace.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Masarai ya kara da cewa gwamnatin jiharsa ta na kashe N1.2 biliyan a kowanne wata wurin biyan tsoffin ma'aikatan kananan hukumomi da na jihar kudin fansho, Daily Nigerian ta ruwaito.

A cewarsa, ya na kokarin ganin ya biya dukkan kudaden fansho da na garatuti da ake bin gwamnati kafin ya kammala mulkinsa.

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mulkinsa ba zai huta ba har sai kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta a yanzu ta kawo karshe, Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari, wanda ya samu wakailcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonayan Onu, ya sanar da haka ne a yayin gabatar da wani littafi mai suna "Standing Strong" wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta a Abuja.

"Muna cigaba da duba hanyoyi da tsarikan cigaba da nakasa dukkan wani karfin 'yan ta'adda a kasar nan," yace.

Kara karanta wannan

Masari ya janye ra'ayinsa kan bindiganci, ya nemi a ayyana dokar ta-baci kan rashin tsaro

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng