Kasar Sin zata bude bankuna a Najeriya, wannan shine yarjejeniyar da mukayi: Jakadan Beijing

Kasar Sin zata bude bankuna a Najeriya, wannan shine yarjejeniyar da mukayi: Jakadan Beijing

  • Gwamnatin kasar China zata budewa bankunanta a Najeriya kuma zasu fara aiki nan ba da dadewa ba, cewar Jakadanta
  • Hakazalika bankunan Najeriya zasu iya bude rassa a kasar Sin kuma su rika gudanar da ayyukansu
  • Jakadan yace wannan na cikin abubuwan da aka amince dasu yayin yarjejeniyar canjin kudi tsakanin Najeriya da Sin

FCT Abuja - Jakadan kasar Sin dake Najeriya, Mr Cui Jianchun, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin kasarsa zata budewa bankuna a Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa hakazalika za'a iya bude bankunan Najeriya a Sin, inda yace wannan na cikin abubuwan da suka wajaba ayi don tabbatar da yarjejeniyar canjin kudi tsakanin Najeriya da Sin ta yiwu.

Jakadan Sin, ya ce yanzu haka yana aiki tukuru don ganin cewa bankuna kasarsa su fara aiki a Najeriya, hakazalika na Najeriya a kasar Sin.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

ThisDay ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja ga manema labaran yayin jawabi kan nasarorin da aka samu kan shirin canjin kudi tsakanin Najeriya da Sin.

Jianchun yace za'a fadada shirin daga N750 billion da akayi a bayan.

Kasar Sin zata bude bankuna a Najeriya, wannan shine yarjejeniyar da mukayi: Jakadan Beijing
Kasar Sin zata bude bankuna a Najeriya, wannan shine yarjejeniyar da mukayi: Jakadan Beijing Hoto: Aso Villa

A cewarsa:

"Manyan bankunan kasashenmu biyu ke aiwatar da yarjejeniya. Ana samun nasara kuma ina kokarin ganin bankunan Sin sun zo Najeriya kuma Najeriya su fara aiki a Sin.

Rahoton ya kara da cewa Jakadan yace zai so yan majalisun Najeriya su fara mu'amala da yan majalisun Sin yayinda ake shirin taron zuba jarin Sin da nahiyar Afrika da zai gudana a Nuwamba a kasar Senegal.

Ma'aikatar Lafiya na shirin karban bashin N82bn don sayen ragar kariya daga cizon sauro

Kara karanta wannan

Bayan shekara 1, Rundunar soji ta ki mayar da Kanal din da ya halaka 'yan Boko Haram 377 bakin aikinsa

A bangare guda, Majalisar dattawar Najeriya ta yi Alla-wadai da shirin da ma'aikatar kiwon lafiyan Najeriya ke yi na karban bashin $200 million (N82,070,388,916.76) a kasafin kudin shekarar 2022.

Ma'aikatar za ta amfani da wannan bashi ne wajen sayawa yan Najeriya ragar kariya daga cizon sauro, rahoton SR.

Sakaraten din-din-din na ma'aikatar ya bayyanawa kwamitin a taron bayani kan kudin da ma'aikatar ta bukata cikin kasafin kudin 2022.

Daya daga cikin mambobin kwamitin kiwon lafiya na majalisar dattawa, Gershom Bassey, ranar Talata ya ce sam ba dashi za'a yi wannan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng