'Yar shekara 14 ta ci kyautar wacce ta kera mutum-mutumin dake taimakawa wajen kiwon lafiya

'Yar shekara 14 ta ci kyautar wacce ta kera mutum-mutumin dake taimakawa wajen kiwon lafiya

  • Wata yar Najeriya, Famidah Yussuf, mai shekaru 14 kacal da haihuwa ta ci kyautar bankin Union na ilmin zamani
  • Famidah Yussuf ce ta zama zakara a Musabaqar kera mutum-mutumin zamani da zai taimaka wajen yin aiki lokacin karancin Malaman jinya da likitoci
  • Yarinyar ta kera mutum-mutumin da nan gaba zai kwace ayyukan Malaman jinya da unguzomomi

Abuja - Wata 'yar Najeriya mai suna Famidah Yussuf ta zama jarumar shekara a musabaqar ilmin kera mutum-mutumin zamani da bankin Union ta shirya.

A jawabin da bankin Union ta saki a shafin LinkedIn, dalibar ta kera mutum-mutumin wanda zai taimaka wajen kula da marasa lafiya idan ana karancin Malaman jinya da Likitoci.

An sanyawa wannan mutum-mutumi suna Famidah.

Kara karanta wannan

Fusatattun jam'an gari sun sheƙe wani ɗan leken asirin yan bindiga da iyalansa a Kaduna

Menene manufar Famidah?

A cewar jawabin, manufar Famidah shine ragewa Likitoci da Malaman jinya aiki wajen tattara bayanan marasa lafiya da bibiyar halin da suke ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yar shekara 14 ta ci kyautar wacce ta kera mutum-mutumin dake taimakawa wajen kiwon lafiya
'Yar shekara 14 ta ci kyautar wacce ta kera mutum-mutumin dake taimakawa wajen kiwon lafiya Photo credit: Union Bank of Nigeria/LinkedIn
Asali: UGC

Ayyukan da mutum-mutumin ke yi?

Mutumi-mutumin mai suna Famidah na iya baiwa marasa lafiya magani, bibiyarsu lokaci bayan lokaci, daukar karfin jikinsu, bugun zuciyarsu, da kuma yanayin hawan jininsu.

A cewar jawabin Union Bank:

""Famidah na taimakawa wajen duba irin gajiyar da marasa lafiya ke yi da kuma kiwon lafiyarsu gaba daya. Muna taya ki murna Famidah."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng