Hotunan wata mata da aka kama da bindiga da harsashi da ɗimbin muggan ƙwayoyi a Delta
- Jami'ar rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta kama wata Blessing Oghule
- An kama ta ne da bindiga da harsashi da kuma miyagun makamai
- Har ila yau, a tare da ita an samu miyagun kwayoyi ciki har da hodar ibilis
Jihar Delta - Rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai sun kama wata Blessing Oghule da bindiga, sauran miyagun makamai da kuma miyagun kwayoyi.
Bisa ruwayar LIB, mai magana da yawun rundunar, DSP Bright Edafe ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
LIB ta ruwaito yadda aka kama Oghule tare da wasu mutane 3 yayin wani samame da rundunar ta kai wurin shaye-shaye a yankin Abraka da ke Asaba.
A cewar kakakin:
“A ranar 21 ga watan Oktoban 2021 da misalin karfe 2:15, bisa umarnin kwamishinan ‘yan sandan jihar Delta, CP Ari Muhammad, rundunar ta kai samame wuraren Abraka a Asaba.”
Kakakin yan sandan ya cigaba da cewa, a wurin an kama mutane 5 da ake zargin barayin waya ne, wata jaka da wani abu da ake zargin hodar ibilis ce da kuma wiwi duk a hannun Oghule.
Yayin samamen, an kama mutane 4, ciki akwai Blessing Oghule, Nweke Abudi, Ebuka Paul da Sunday Inuse.
A hannun su an samu bindiga karama, miyagun makamai 5, wayoyi 5 da ake zargin na sata ne, wata jaka mai dauke da wani abu mai kama da wiwi.
Har ila yau a cikin jakar akwai wata leda wacce ake zargin hodar ibilis ce a ciki duk daga hannun Blessing Oghule.
An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba
Wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.
Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.
An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.
Asali: Legit.ng