EFCC ta taso Sakataren gwamnatin Jonathan a gaba kan zargin badakalar miliyoyin kudi

EFCC ta taso Sakataren gwamnatin Jonathan a gaba kan zargin badakalar miliyoyin kudi

  • A ranar Lahadi ne Hukumar EFCC ta tsare tsohon SGF, Sanata Anyim Pius Anyim
  • Binciken Stella Oduah ya jawo aka taso sakataren na gwamnatin Jonathan gaba
  • Oduah ta tura miliyoyi zuwa wani kamfaninsu Anyim a lokacin da ta ke Minista

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta tsare Sanata Anyim Pius Anyim kan zargin wata badakala.

Jaridar Daily Trust tace ana zargin tsohon sakataren gwamnatin tarayyar da hannu a badakalar da ake zargin Sanata Stella Oduah ta tafka a gwamnati.

A lokacin da Stella Oduah ta ke rike da Ministar harkokin jiragen sama, ana zargin ta yi gaba da makudan kudi da sunan za ta saye wasu motocin hawa.

Hakan ta sa Anyim Pius Anyim ya shafe sa’o’i a hannun jami’an EFCC inda aka rika yi masa tambaya a kan wadannan kudi da suka shiga kamfaninsu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan harin yan ta'adda, jirgin kasan Abuja/Kaduna zai koma aiki ranar Asabar

Inda Anyim ya shgia matsala

Kamfanin da kudin da ake zargin Oduah ta wawura sun fada asusun wani kamfani da Pius Anyim yana cikin darektocinsa, don haka aka tsare shi jiya.

Anyim Pius Anyim
Anyim Pius Anyim Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Rahotanni daga Punch sun ce tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya dauki sama da sa’o’i shida yana amsa tambayoyi kan binciken a babban ofishin EFCC.

Har zuwa cikin dare a ranar Lahadi, 24 ga watan Oktoba, 2021, Anyim Pius Anyim bai bar hannun EFCC. Wasu suna tunanin babu mamaki a nan ma ya kwana.

“Bincike ya nuna daga cikin N780m ma’aikatar harkokin jirage da aka yi gaba da su, an ga wasu a cikin kamfanin da Sanata Anyim ne darektansa.”

Pandora Papers

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa suna binciken wadanda sunayensu ya bayyana a Pandora Papers.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Shugaban NHRC da sauran manyan lauyoyi 71 da suka samu girmamawa ta SAN

Tsohuwar Ministar harkokin jiragen tana cikin wadanda badakalarsu ta fito a jerin Pandora Papers.

Hukuncin Ken Saro Wiwi

Dazu aka ji cewa shekara da shekaru da hukunta Ken Saro-Wiwa, Najeriya za ta yafe masu laifinsu. Muhammadu Buhari ya fara duba yiwuwar yi masu afuwa.

Shugaban kasa ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da dattawan kasar Ogoni da suka kai masa ziyara a fadar shugaban kasa na Aso Rock Villa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng