Wata sabuwa: Haramun ne mutum ya bada sadaqan Naira N10 a wurin ibada, Malamai

Wata sabuwa: Haramun ne mutum ya bada sadaqan Naira N10 a wurin ibada, Malamai

  • Wani mabiyin addinin kirista, Johnson Austin, ya bayyana cewa haramun ne mutum ya bada sadaqar N10 a wurin ibada
  • Wasu daga cikin malaman addinin kirista da sauran mabiya sun nuna cewa sadagar N10 ko N5 tamkar cin mutunci ne
  • Hakanan yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan darajan kuɗin da kuma abinda zasu iya siya a halin yanzu

Calabar, Cross River - Wani mamba a cocin denominational dake Calabar, jihar Cross Ribas, Johnson Austin, yace laifi ne ka bada tallafin Naira N10 a coci.

Autin ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake bada gudummuwarsa a rahoton da Dailytrust ta haɗa kan darajar kuɗi ta N10 da kuma N5.

"Idan mutum zai yi rowar kuɗi, sai ya yi wa Ubangiji?" Autin ya yi wannan tamabyar yayin da yake jawabi.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Miyagun yan bindiga sun ƙone fadar basaraken gargajiya a Najeriya

Naira goma
Wata sabuwa: Haramun ne mutum ya bada sadaqan Naira N10 a wurin ibada, Malamai Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shi kaɗai ke da irin wannan tunanin?

Da yawa daga cikin mabiya addinin kiristanci da kuma malaman coci a Calabar, babban birnin jihar Cross Ribas, sun bayyana damuwarsu kan mutanen dake bada sadaqar N10 ko N5 a coci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsu, wannan rashin godiya ne da kuma rashin girmama Ubangiji mutum ya bda sadaqar waɗannan kuɗaɗen, waɗanda sam ba su da daraja a yanzu.

Hakanan a wajen cocin, mutane da dama sun koka kan yadda mutane ba su son tallafawa addinin su a Najeriya.

Me mutane suke cewa?

A mafi yawancin kasuwannin cikin birnin Calabar, da wuya ka samu abubuwan da N10 da N5 zasu iya siyan maka a halin yanzun.

Wata matar aure, Margaret Akpan, tace:

"Faɗamun abinda zaka iya siya a kasuwa da wannan kuɗin a yanzu? ko alewar yara da Tom-Tom zai wahala kasame su a haka."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kira wayar wani a coci, ya fito sun bindige shi sun gudu

"Wasu mutane na ganin cin mutunci ne ka basu kyautar N10 ko N5. In gajerce muku zance a kwanankin nan waɗan nan takardun kuɗin ma ba su yawo sosai."
"Ina da tabbacin nan gaba kaɗan zasu ɓace a daina amfani da su kamar yadda tsaba ta ɓace, amma a wasu kasashen kamar Africa ta yamma ana amfani da kuɗin tsaba har yanzu."

A wani labarin kuma Cikin mako ɗaya, Miyagun yan bindiga sun hallaka Sarakuna biyu da wasu mutum 45 a Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa adadin fararan hula da mahara suka kashe ya linka biyu idan aka kwatanta da na wancan makon.

Sai dai a ɗaya ɓangaren kuma an samu saukin yawaitar hare-hare, amma harin Sokoto shine ya fi muni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: