Dakarun sojoji sun yi arangama da matasa a Imo, an ƙone gidaje da dama
- Sojojin Nigeria sun yi arangama da matasan garin Etekuru da ke karamar hukumar Ohaji a Imo
- Sojojin sun kai hari garin ne sakamakon kashe wani abokin aikinsu da aka yi a baya-bayan nan aka sace bindigarsa
- Mutane da dama sun tsere daga gidajensu sakamakon harin inda sojojin suka kone gidaje da dama
Imo - Hankulan mutane ya tashi a garin Etekuru, a karamar hukumar Ohaji ta jihar Imo a ranar Laraba a yayin da dakarun sojoji da matasan garin suka yi arangama, SaharaReporters ta ruwaito.
Jaridar The Punch ta ruwaito tunda farko cewa an tare wani soja an kashe shi sannan an sace bindigarsa.
A wani lamari mai kama da mayar da martani, sojojin sun shiga garin sun kona gidaje.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rikicin na zuwa ne makonni biyu bayan sojoji sun yi fada da matasa a Izombe, karamar hukumar Oguta na jihar ta Imo.
Harin ya yi sanadin rasuwar mutane uku, ciki har da sojoji guda biyu da kona gidaje masu yawa a garin.
Rikicin na baya-bayan nan ya tada hankulan al'ummar garin, ya tilastawa wasu da dama tserewa daga gidajensu.
Yan bindiga sun halaka sarakuna biyu a Imo
Wasu 'yan bindigan a ranar Talata sun kai wa masu sarautan gargajiya hari a hedkwatar karamar hukumar Njaba inda suka kashe guda biyu nan take.
Rundunar yan sandan jihar Imo ta fitar da sanarwa inda ta bayyana sunayen sarakunan da aka kashe kamar haka Mai martaba Eze S.C. Osunwa na Ihebinowere da Mai marbata Eze Barr A. E Durueburuo na Okwudor.
Yan sandan sun kuma bayyana cewa Mai martaba Eze A. N. Onyeka na garin Nkume ya samu raunuka sakamakon harbinsa da aka yi da bindiga.
'Yan sanda sun yi ram da baƙin haure 2 dauke da abubuwa masu fashewa cikin jakunkuna
A wani rahoton, rundunar ‘yan sandan yankin Akwa-Ibom sun samu nasarar damkar wasu ‘yan kasar waje 2 da abubuwa masu fashewa kamar yadda ya zo a rahoton Channels TV.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Odiko Mcdon ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Talata a hedkwatar ‘yan sanda da ke Uyo, babban birnin jihar.
Jaridar ta ruwaito cewa wadanda ake zargin sun hada da Adede De Black, Fombutu da Benard Mfam daga karamar hukumar Ikom da ke jihar Cross River.
Asali: Legit.ng