Kano: Muhuyi ya bukaci babbar kotu da ta haramtawa 'yan sanda kama shi

Kano: Muhuyi ya bukaci babbar kotu da ta haramtawa 'yan sanda kama shi

  • Barista Muhuyi Rimingado, dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa a Kano ya maka hukumar 'yan sanda a kotu
  • Ya bukaci wata babbar kotun tarayya da ke Kano da ta haramta musu kama shi kafin a kammala shari'ar
  • Mai shari'a Jane Inyang ya bukaci a aikewa wadanda ake kara tsammaci sannan su bayyana a gaban kotu ranar 3 ga Nuwamba

Kano - Dakataccen shugaban hukumar sauraron korafin jama'a da yaki da rashawa na jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya bukaci wata babbar kotun tarayya da ke Kano da ta hana 'yan sanda kama shi.

Sai dai kuma, kotu da ke samun shugabancin Mai shari'a Jane Inyang, a ranar Laraba ta umarci wadanda ake kara, da suka hada da 'yan sanda tare da kakakin majalisar jihar da su bayyana a gaban ta.

Kara karanta wannan

An daure dalibai 19 da aka kama sun shiga kungiyar asiri a Jami’a bayan doguwar shari'a

Daily Trust ta ruwaito cewa, kotun ta na son jin dalilin da zai sa kada ta karba bukatar tsohon shugaban hukumar yaki da rashawan na jihar.

Kano: Muhuyi ya bukaci babbar kotu da ta haramtawa 'yan sanda kama shi
Kano: Muhuyi ya bukaci babbar kotu da ta haramtawa 'yan sanda kama shi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda lauyan Rimingado, Barista Muhammad Dan'azumi ya mika bukata a gaban kotun, ya ce bukatarsu ta hana wadanda suka yi kara kama Rimingado ta samu goyon baya daga sakin layi 44 na rantsuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zahradeen Magaji Rimingado, dan tsohon shugaban hukumar yaki daa rashawan ne ya ke bukatar a hana mutum shidan kama mahaifinsa har sai an kammala shari'ar tare da yanke hukunci.

A yayin mika bukatar gaban kotun, Barista Dan'azumi ya bukaci kotun da ta hana dukkan wadanda ake karar daga kama wanda ya ke karewa, inda ya ce akwai wata umarni daga babbar kotun jihar Kano wacce ke samun shugabancin Mai shari'a Sanusi Ado Magaji wacce ta hana su kama shi.

Kara karanta wannan

Muhyi: Kotu ta bukaci ganin kakakin majalisar jihar Kano da wasu mutane 5

Alkalin wanda ya bukaci a mika takardar kira ga wadanda ake karar, ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 3 ga watan Nuwamba, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan sandan Kano sun cafke masu kai wa 'yan bindiga man fetur har Katsina

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kano sun cafke wasu mutum biyu da ake zargin suna samarwa da 'yan bindigan jihar Katsina man fetur daga Kano.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, DSP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Talata a Kano, Daily Nigerian ta wallafa.

Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Musbahu Rabi'u mai shekaru 31 da kuma Jamilu Abdullahi mai shekaru 37, dukkansu mazauna karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: