Gwamnatin Buhari ta dauki nauyin Daliban Chibok 57, sun fara karatun Digiri a Jami’ar Atiku

Gwamnatin Buhari ta dauki nauyin Daliban Chibok 57, sun fara karatun Digiri a Jami’ar Atiku

  • ‘Yan matan Chibok da aka ceto sun soma karatun digiri a jami’ar AUN
  • Wani jami’in makarantar, Dan Okereke ya tabbatar da haka a makon nan
  • Okereke yace yaran suna cikin sababbin shiga jami’ar na shekarar bana

Adamawa - Wasu daga cikin ‘yan makaratar sakandare ta Chibok da aka ceto daga hannun Boko Haram sun samu damar yin karatu a jami’ar AUN.

Jaridar Daily Trust tace wadannan Bayin Allah za su yi karatu a jami’ar ta American University of Nigeria watau AUN da ke garin Yola,a jihar Adamawa.

Darektan sadarwa na jami’ar, Mista Dan Okereke, ya tabbatar da cewa ‘yan mata 57 daga makarantar Chibok suna cikin wadanda suka shigo AUN.

Wadannan yara sun shigo ajin farko, sun soma karatun digiri a jami’ar mai tsarin karatun Amurka.

Wasu daga cikin ‘yan matan da suka shigo wannnan babbar jami’a ta zanta da manema labarai, ta kuma bayyana irin farin ciki na samun wannan dama.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da baƙin haure 2 dauke da abubuwa masu fashewa cikin jakunkuna

Daliban Chibok
Buhari da yaran Chibok Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cewar wannan sabuwar dalibar, wannan wata dama ce wanda ta dade tana jiran irin ta a rayuwa.

“Jami’ar AUN ta shirya bikin tarbar sababbin dalibai na bana, daga ciki har yaran Chibok 57 da yanzu sun zama ‘yan mata da suka shigo aji daya.” - Okereke.

Margee Ensign ta yi magana

Shugaban jami’ar AUN, Margee Ensign mai shekara 67 tayi kira ga sababbin shigowar su yi amfani da ilminsu domin magance matsalolin Duniya.

Ensign tace mutane suka jawo matsalolin da ake fama da su, kuma ‘Dan Adam zai iya kawo mafita.

“Ko matsalar sauyin yanayi ne, kiwon lafoya, rigingimu, rashin adalci, sha'anin jinsi, duk ana iya kawo karshen matsalolin da muka jawo.” - Margee Ensign.

Rashin tsaro a jihar Kaduna

A makon nan ne aka ji Sarkin Birnin Gwari, Mai martaba Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, ya yi magana kan halin da 'yan bindiga suka tsinci kansu a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

‘Yan wasan Kannywood sun kirkiri fim a kan rikicin Boko Haram a Arewacin Najeriya

Zubairu Jibril Mai Gwari yana magana ne bayan matakan da gwamnatin jihar ta dauka na datse layukan sadarwa, yace 'yan bindiga suna neman abin da za su ci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng