Yanzu-yanzu: Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar EndSARS da barkonon hayaki
- Jami'an tsaro sun watsawa matasa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa
- Wannan biyo gabayn gargadin da kwamishanan yan sanda yayi
- An damke mutane da dama cikin wadanda suke gudanar da zanga-angar
Lekki - Jami'an yan sanda a ranar Laraba sun tarwatsa matasan dake zanga-zangar tunawa da EndSARS dake gudana a Lekki Toll Gate, jihar Legas.
Jami'an yan sandan sun watsawa matasan barkonon hayaki wanda aka fi sani da Tiya Gas don tarwatsa taron, rahoton ChannelsTV.
A yanzu matasan sun gudu daga wajen.
Hotunan yadda 'yan sanda suka yi ram da masu zanga-zanga a Lekki Tollgate
Yan sanda sun yi ram da mutanen da ke zanga-zanga a Lekki tollgate a Legas.
Duk da jan kunnen da aka yi wa masu son yi tattakin cika shekara daya da yin asalin zanga-zangar, sun fito kwan su da kwarkwatarsu.
A safiyar Laraba, wasu mutane sun taru a tollgate inda jami'an tsaro a shekarar da ta gabata suka tarwatsa taron.
Hakeem Odumosu, kwamishinan 'yan sandan jihar Legas tun farko ya ce jami'ansa su bar ababen hawa ne kadai a yankin Lekki ba wata zanga-zanga ba.
Tuni ya tura jami'an tsaro inda suka mamaye wurin.
Asali: Legit.ng