Babu dan Najeriya mai tunanin da zai sake shiga zanga-zangar EndSARS, Hedkwatar Tsaro

Babu dan Najeriya mai tunanin da zai sake shiga zanga-zangar EndSARS, Hedkwatar Tsaro

  • Matasa a fadin Najeriya sun taru dan tunawa da ranar 20 ga Oktoba 2020
  • Da safiyar Laraba an damke mutane da dama da suka fita zanga-zangar
  • Daga cikin wadanda aka damke akwai wakilin Legit.ng Abisola Alawode

Yayinda yan fafutuka ke zanga-zangar shekara daya da gudanar #EndSARS yau Laraba, hedkwatar tsaro ta bayyana cewa babu mai tunanin da zai sake bari abinda ya faru bara ya sake ritsawa da shi.

Diraktan yada labarai na DHQ, Manjo Janar Benjamin Saywerr, ya bayyana hakan ya TheNation.

Yace dubi ga irin asarar rayuka da dukiya da aka yi bara, babu wani mai hankalin da zai sake fita zanga-zanga.

A cewarsa:

"Kana ganin irin abinda mutane suka fuskanta lokacin zanga-zangar a baya na sace-sace, lalata dukiyar mutane, kone-konen gidaje, kashe-kashen yan sanda da bari batagari na cin zarafin mutane yadda suka ga dama, wani mai tunani zai saurari masu kira ga wannan taro?"

Kara karanta wannan

EndSARS: Yan sanda sun damke dan jaridar Legit a LekkiToll Gate

"A yanzu ina ganin kan mutane ya waye kuma ba zasu yarda wani ya rudesu ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babu dan Najeriya mai tunanin da zai sake shiga zanga-zangar EndSARS, Hedkwatar Tsaro
Babu dan Najeriya mai tunanin da zai sake shiga zanga-zangar EndSARS, Hedkwatar Tsaro Hoto: DHQ
Asali: Twitter

Yan sanda sun damke dan jaridar Legit a LekkiToll Gate

Jami'an yan sandan Najeriya a ranar Laraba, 20 ga Oktoba sun damke dan jaridar Legit.ng, Abisola Alawode, a filin tunawa da ranar zanga-zangar EndSARS a Oktoba 2020.

An damke Abisola ne a filin Lekki Toll Gate inda zanga-zangar ke gudana.

Abisola, wanda aiki ya kaisa wajen na kawo mana rahoto ne kan abubuwan dake gudana lokacin da yan sanda sukayi ram da shi.

Yan sanda sun bukaci yan jaridar su rataye katin shaidarsu kuma yana shirin haka kenan suka kwace kamarori da kayan aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng