Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun harbe sarakuna biyu har lahira a wurin taro

Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun harbe sarakuna biyu har lahira a wurin taro

  • Wasu bata gari da ba a san ko su wanene ba sun kai wa sarakuna hari yayin taro a Imo
  • 'Yan bindigan sun halaka sarakuna biyu nan take yayin da saura suka samu rauni daban-daban
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar Imo, Mike Abattam ya tabbatar da afkuwar lamarin

Jihar Imo - Masarautun gargajiya a jihar Imo sun shiga zaman makoki sakamakon kashe wasu sarakuna biyu da aka yi.

Daily Trust ta ruwaito cewa sarakunan biyu sun tafi hallartar taron masu ruwa da tsaki ne a Nnenasa, hedkwatar karamar hukumar Njaba na jihar a lokacin da bata garin suka kai hari.

Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun harbe sarakuna biyu har lahira a wurin taro
Taswirar Jihar Imo. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Sarakunan da abin ya shafa sune Eze E. A Durueburuo, Obi I na Okwudor, da Eze Sampson Osunwa na garin Ihebinowere.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bam ya hallaka akalla mutum 32 a Masallacin Shi'a a ​kasar Afghanistan

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton na Daily Trust ya kuma bayyana cewa wasu masu rike da sarautun gargajiyar sun bar wurin da raunuka daban-daban.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Imo, Mike Abattam ya tabbatar da rasuwar sarakunan biyu.

Ya ce an tabbatar da mutuwarsu nan take a wurin yayin da wadanda suka jikkata kuma an garzaya da su asibiti domin basu kulawan likitoci.

Gwamnan Imo Hope Uzodinma ya yi Allah-wadai ta harin

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, yayin hira da ya yi da Channels Television ya yi tir da kisar ya kuma jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.

Ya yi alkawarin za a gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu a kuma hukunta su daidai da laifinsu.

Har wa yau, gwamnan ya yi kira ga al'ummar jiharsa su kwantar da hankulansu domin gwamnati tana bin didigin lamarin.

Kara karanta wannan

Jarumin Gwamna El-Rufai ya bayyana abinda ke matukar tsorata shi

Harin shine na baya-baya cikin muggan hare-hare da ake kai wa a jihohin kudu maso gabas.

A ranar Lahadi, yan bindiga sun kai hari hedkwatar yan sanda a jihar Ebonyi sun kashe jami'i daya sun kona motoccin sintiri.

Ana alakanta hare-haren na baya-bayan da kungiyoyin masu neman ballewa daga Nigeria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164