Annabi na kowa ne: Faston da ya jagoranci kiristoci zuwa shagalin bikin Maulidi a Kaduna

Annabi na kowa ne: Faston da ya jagoranci kiristoci zuwa shagalin bikin Maulidi a Kaduna

  • Kiristoci, ciki har da fastoci sun taya musulmai murnar shagalin maulidi a jihar Kaduna
  • Babban faston wata coci da ke Sabon Tasha, Yohanna Buru ne ya jagoranci kiristocin wurin shagalinbirnin jihar
  • Babban faston wata coci dake Sabon Tasha, Yohanna Buru ne ya jagoranci kiristocin wurin shagalin

Jihar Kaduna - Kiristoci sun taya musulmai shagalin bikin Maulidi, haihuwar Annabi Muhammadu, SAW a jihar Kaduna a ranar Talata kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.

Mabiyan addinan biyu sun taru ne a Ranchers Bees Stadium da ke birnin jihar, inda ya ce taron zai taimaka wurin karfafa zumunci tsakanin addinai da al’adun.

Fasto ya jagoranci kiristoci zuwa wurin shagalin bikin Maulidi a Kaduna
Fasto a wurin taron Maulidi a Kaduna. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shugaban fastocin Christ Evangelical Intercessory Fellowship Ministries, Sabon Tasha, Fasto Yohanna Buru ne ya jagoranci Kiristocin wurin shagalin murnar haihuwar annabi Muhammad SAW.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

Annabi na kowa ne kuma zaman lafiya ya koyar tsawon rayuwarsa

Ya bayyana cewa:

“Annabi na kowa ne komin addinin ka, al’ada, kala da kuma yanki a duniya, kuma ya na yin wa’azi akan zaman lafiya tsawon rayuwar sa.”

Ya kula a matsayin sa na mai yada zaman lafiya da kuma malamin addinin kirista, inda ya ce ya na taya musulmai murna duk da hakan bai canja imaninsa ba.

Ya bayyana yadda lokacin bikin kirsimeti musulmai daga bangarori daban-daban na arewacin Najeriya su ka je coci taya su murna.

Fasto ya yi kira ga 'yan Nigeria sun hada kai

Ya bukaci ‘yan Najeriya su yi kokarin ganin sun yada zaman lafiya, kauna da hadinkai a fadin kasar nan.

Buri ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga uku: Rukunin karshe na sabbin jiragen yaƙin 'Super Tucano' sun iso Najeriya

“Wajibi ne mu gane cewa mu ‘ya’yan Adam da Hauwa’u ne. Mu ‘yan uwa mata da maza ne kuma duk mun yi imani da Al’Qur’ani da Bible kuma mun yarda da rayuwa bayan mutuwa, don haka mu zama ma su kauna juna.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: