Jerin sunaye da ma'aikatu: Matawalle ya ƙirƙiri sabbin ma'aikatu 4, ya sauya wa kwamishinoni wurin aiki
2 - tsawon mintuna
- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya amince da kafa wasu ma’aikatu 4 na daban a jihar
- Bayan kafa ma’aikatun ya kuma zabo sabon kwamishina ga ko wacce sabuwar ma’aikata
- Ya kafa ma’aikatar kula da dajika da dabbobin kiwo, da ta samar da dukiya da ayyukan yi da sauran biyu
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya tabbatar da samar da ma’aikatu 4 sannan ya zabo sababbin kwamishinoni na ma’aikatun.
Ya bayyana hakan ne ta wata takarda wacce sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe ya bayyana a Gusau ranar Litinin bisa ruwayar The Punch.
A cewar Balarabe, ma’aikatun da ya kafa guda 4 su ne:
- Ma’aikatar kula da dazuka da bunkasa kiwon dabobbi
- Ma’aikatar samar da dukiya da kuma samar da ayyuka.
- Ma’aikatar yawon bude ido da kula da otal da kuma
- Ma’aikatar gina gidaje da bunkasa birane
Balarabe ya bayyana yadda gwamnatin ta nada sababbin kwamishinoni wadanda za su fara aiki daga nadin.
Ya lissafo ma’aikatun da kwamishinonin kamar haka;
- Ahmed Anka - Ma’aikatar ilimin kimiyya da fasaha
- Abubakar Dambo - Ma’aikatar harkokin kananun hukumomi
- Muh’d Magaji - Ma’aikatar al’adu
- Nasiru Masama - Ma’aikatar matasa da bunkasa wasanni
- Abdulaziz Nahuce - Ma’aikatar ayyuka na musamman
- Zainab Gummi - Ma’aikatar ilimi.
- Sufyan Yuguda - Ma’aikatar kudi
- Fa’eka Marshal - Ma’aikatar harkokin jin kai da annoba
- Rabiu Gusau - Ma’aikatar ayyuka da tafiye-tafiye
- Yazeed Fulani - Ma’aikatar sana’o’i da ma’aikatu
- Ibrahim Gusau - Ma’aikatar dazuka da bunkasa kiwon dabbobi
- Nuradden Gusau - Ma’aikatar ma’adanai
- Junaidu Kaira - Ma’aikatar shari’a
- Akwai Ibrahim Magayaki - Ma’aikatar noma
- Ibrahim Dosara - Ma’aikatar labarai
- Yahaya Gora - Ma’aikatar ilimin gaba da sakandare
- Yahaya Kanoma - Ma’aikatar samar da ayyuka da bunkasa arziki
- Lawal Badarawa - Ma’aikatar bunkasa al’umma
- Sheikh Jangebe - Ma’aikatar harkokin addini
- Aliyu Tukur - Ma’aikatar kasafi da tsari,
- Aliyu Tsafe - Ma’aikatar lafiya,
- Mamman Tsafe - Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida,
- Abubakar Tsafe - Ma’aikatar yawon bude ido da kula da otal
- Ibrahim Mayana - Ma’aikatar ruwa
- Abubakar Bore - Ma’aikatar bunkasa kauyaku.
Asali: Legit.ng
Tags: