Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba
- A 2019 shugaba Muhammadu Buhari ya kakkabe rahoton kwamitin Steven Oronsaye
- Shugaban kasa ya bada umarni ayi aiki da shawarwarin da Oronsaye ya bada a 2012
- Ba a fara dabbaka wadannan matakai da za su sa gwamnati ta rage kashe biliyoyi ba
Abuja - Gwamnatin tarayya ba ta fara aiki domin dabbaka rahoton da kwamitin Steven Oronsaye ya taba gabatar wa a lokacin Goodluck Jonathan a 2012 ba.
Jaridar Daily Trust tace hakan na zuwa ne duk da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kakkabe wannan rahoto, ya bada umarnin ayi aiki da shi.
Gwamnatin Najeriya tana kukan cewa abin da ta ke kashe wa duk shekara a kan ma’aikatan gwamnatin tarayya ya yi yawa, don haka ake ta neman mafita.
Wannan rahoto zai yi garambawul a kan ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati a kasar nan.
An dawo da aikin Steven Oronsaye
A watan Afrilun 2021, shugaba Muhammadu Buhari ya fito ya shaida wa Duniya cewa zai yi amfani da shawarar kwamitin Oronsoye domin a rage facaka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wancan lokaci, Ministar kudi da tattalin arziki, Zainab Ahmed ta tabbatar da cewa hakan zai jawo a hada wasu ma’aikatun su zama daya, amma har yau shiru.
Shugaban hukumar BPSR mai kokarin gyara aikin gwamnati, Dasuki Arabi yace shugaban kasa ya kai maganar aikin kwamitin Oronsaye gaban majalisar FEC.
A 2016, kafin Dr. Joe Abah ya bar kujerar BPSR, ya sauya fasalin kwamitin da za su yi wannan aiki. Daily Trust tace kawo yanzu, babu wani hobbasa na kwarai.
Lamarin na neman zama shiririta?
Da aka tuntubi sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a kan wannan batu, sai ya yi gum. Willie Bassey ya bukaci ‘yan jarida su ji ta bakin Ministar kudi.
Mai magana da yawun Ministar kudin Najeriya, Yunusa Abdullahi yace ana aiki kan dabbaka wannan rahoto, yace har an kafa kwamiti da zai gabatar da rahoto.
Sai dai shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan, tana ganin sam ba zai yiwu a dabbaka shawarar wannan rahoto da ya dade a kwance ba.
Malaman jami'a suna kuka da IPPIS
A yau ne aka ji Gwamnatin tarayya ta bayyana abin da ya faru wasu malaman jami’a ba su karbar albashi bayan shiga manhajar IPPIS da ASUU ta ke adawa da ita.
Akawun Gwamnati yace laifin malamai ne da suka ki rajista da manhajar IPPIS da wuri. Baya ga haka, ana zargin malaman da bada bayanan bogi da ake yin rajista.
Asali: Legit.ng