An yi da Jana'izar Hajiya Aminatu Bintu matar marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gummi
- An bizne matar marigayi Sheikh Abubakar Gumi da ta rasu ranar Asabar
- Manyan Malamai da jagororin siyasa sun samu damar halartan jana'izar
- Ta rasu ta bar 'yaya takwas cikinsu akwai Birgediya Janar AbdulKadir
Kaduna - An gabatar da Jana'izar Hajiya Aminatu Bintu Muhammad Bello matar marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gummi.
An yi jana'izar ne bayan Sallar La'asar a gidan Sheikh Abubakar Mahmud Gumi dake No 1 Modibbo Adama Road, Unguwar Sarki Kaduna.
Hadimin Dr Ahmad Gumi, Salisu Hassan Webmaster, ya bayyana cewa Dr. Hamza Abubakar Mahmud Gumi wanda dayane daga cikin yayan da ta haifa shine ya jagoranci mata sallah.
A cewarsa, cikin wadanda suka halarci Janazar akwaiDr. Sulaiman Adam Limamin Sultan Bello, Sheikh Balele Wali, Alkali Tahir Lawal Abubakar, Malam Murtala Shanono, Mal Nuhu Alhafiz, Mal Isah Abdullahi Adarkake, Malam Bello Sarkin Malam da Limamin Masallacin Danja Zaria da sauran su.
Daga cikin manyan kasa da suka halarta sun hada Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufai, mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, Sanata Ahmad Muhammad Makarfi, da Sanata Musa Bello.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
'Yayan da ta bari
Ta rasu tana da shekaru 86 ta bar 'ya'ya guda takwas maza hudu mata hudu wanda suka hada da:-
Dr. Hamza Abubakar Gumi
Brig. Gen. Abdulkadir Abubakar Gumi
Malam Hassan Abubakar Gumi
Malam Yusuf Abubakar Gumi
Hajiya Ummulkhair Abubakar Gumi
Hajiya Aisha Abubakar Gumi
Hajiya Hauwa Abubakar Gumi
Hajiya Baraka Abubakar Gumi
Hajiya Amina wacce mahaifiya ce ga Brig. Gen. Abdulkadir Abubakar Gumi ta rasu bayan ta yi jinya na 'yan kwanaki a Asibitin Sojoji na 44 dake garin Kaduna.
Asali: Legit.ng