Yajin-aiki: Sai Majalisa ta kawo dokar hana yaran mala’u yin Digiri a Jami’o’in waje inji ASUU

Yajin-aiki: Sai Majalisa ta kawo dokar hana yaran mala’u yin Digiri a Jami’o’in waje inji ASUU

  • Kungiyar ASUU ta bada shawarar yadda za a magance matsalar yajin-aiki a saukake
  • Shugaban ASUU yana so a kawo dokar da za ta hana yaran manya yin karatu a waje
  • Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi kira ga majalisar tarayya ta yi doka a kan wannan

Nigeria - Kungiyar ASUU ta malaman jami’a tayi kira ga manyan gwamnatin Muhammadu Buhari su cire ‘ya ‘yansu daga makarantun da ke kasashen waje.

ASUU ta na so manyan kasar su sa ‘ya ‘yansu a makarantun gida tare da sauran ‘yan ya-ku-bayi.

Daily Trust tace kungiyar malaman jami’an ta bukaci majalisar tarayya ta kawo doka da za ta wajabta wa masu rike da mukamai hana kai ‘ya ‘yansu waje.

Kungiyar ta ASUU tace yin haka zai sa masu rike da madafan iko da juya akalar gwamnatin kasar su san yadda abubuwa suka tabarbare a makarantun na gida.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Shugaban kungiyar ASUU ta kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana haka a lokacin da suka cigaba da zama da wakilan gwamnatin tarayya a birnin Abuja.

Jaridar tace Ministan kwadago na tarayya, Sanata Chris Ngige ya jagoranci bangaren gwamnati da nufin a hana malaman jami'an sake shiga wani yajin-aikin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hanan Buhari
Yar shugaban kasa ta gama Jami'a a Turai Hoto: news.obiaks.com
Asali: UGC

Da yake magana a bayan-labule da wakilan da gwamnati ta turo, Farfesa Osodeke yace zai yi kyau a tilasta duk wanda ke gwamnati ya bar ‘ya ‘yansa a Najeriya.

Jawabin Farfesa Osodeke a taron Abuja

“Muna sa rai gwamnati za ta maida shi dole, idan ka karbi kujerar gwamnati, ya wajaba ‘ya ‘ya 'yanka su halarci jami’oin Najeriya.”
“Dole majalisar tarayya ta kawo doka da za ta ce muddin aka ba ka wani mukami, sai dai ‘ya 'yanka su yi karatunsu a nan gida.”

Kara karanta wannan

Sakin Nnamdi Kanu zai kawo ƙarshen rashin tsaro a kudu maso gabas, Sanata Ubah

“Idan har ka san ba za ka yarda yaran ka su tsaya a makarantun gida ba, ka da karbi tayin gwamnati.” – inji Emmanuel Osodeke.

Farfesan yace idan aka yi haka, yajin-aikin da suke zuwa zai taba shafaffu da mai, har a magance matsalar. A karshe ya yi tir da kason da aka ware wa ilmi a 2022.

NPS: INTELS ya dawo ta bayan fage

A makon nan ne mu ka samu wani rahoto da yace akwai yiwuwar Gwamnatin Tarayya ta sake ba kamfanin INTELS kwangilar tsaron jirage a tashoshn ruwan Najeriya.

Tsohon kamfanin na su Atiku Abubakar (a da) ya samu makudan kudi daga NPA tsakanin 2013 da 2019. A 2020 hukumar NPA ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninta da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng