Tsohon Gwamna Ya Rasu bayan Ya yi Fama da Rashin Lafiya
- Gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya yi alhinin rasuwar tsohon gwamnan soji na farko na Jihar Ondo, Kyaftin Ita David Ikpeme
- Marigayi Ikpeme ya rasu yana da shekara 89 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda iyalansa suka tabbatar a makon nan
- Gwamna Aiyedatiwa ya yabawa gudunmawar da Ikpeme ya bayar wajen gina tubalin ci gaban Jihar Ondo tun daga 1976 zuwa 1978
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - Gwamnan Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya nuna alhini tare da mika ta’aziyya ga iyalan tsohon gwamnan soji na farko na jihar, Kyaftin Ita David Ikpeme.
Ikpeme ya zama gwamnan farko na Jihar Ondo a lokacin da aka kirkiro jihar daga tsohuwar jihar Yammacin Najeriya a ranar 3 ga Fabrairu, 1976, karkashin mulkin Janar Olusegun Obasanjo.
Iyalan marigayin sun sanar da rasuwarsa ne ga gwamna Aiyedatiwa a wata wasika da Iquo Ikpeme ya sanya wa hannu kamar yadda Ebenezer Adeniyan ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gudunmawar Ikpeme ga jihar Ondo
Gwamna Aiyedatiwa ya yaba wa marigayin kan gagarumin gudunmawar da ya bayar wajen gina jihar tun lokacin da aka kirkirota.
Ya bayyana Ikpeme a matsayin jajirtaccen jagora, hazikin mai mulki, da kuma ginshiki a garinsa na haihuwa watau Kalaba a Jihar Cross River.
Ondo za ta ta tallafi jana'izar Ikpeme
Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata domin ganin an yi wa marigayin jana’iza mai kyau.
Tribune ta wallafa cewa gwamnan ya yi addu’a Allah ya jiƙan marigayin, ya kuma ba iyalansa ƙarfin gwiwa da juriya.
Ikpeme ya zamo gwarzo a jihar Ondo
Gwamna Aiyedatiwa ya ce jama’ar Jihar Ondo za su ci gaba da tuna irin gudunmawar da Ikpeme ya bayar wajen kafa harsashin ci gaban jihar a matsayin gwamnan farko.
Ya ce tarihin Ikpeme zai kasance abin alfahari ga jihar da kuma al’ummar Najeriya baki ɗaya saboda ayyukan kirki da ya yi.
'Yan jam'iyyar APC sun yi hadari a Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya ziyarci wasu 'yan jam'iyyar APC da suka yi haɗari a asibiti a kwanaki.
Mutanen sun yi hadari ne yayin da suka fito daga ƙaramar hukumar Ilaje domin halartar wani yakin nema zabe da APC ta shirya a Akure.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng