Matar Aure Ta Koma Cizon Yatsa Bayan Ta Siyar Da Kadarorinta Ta Koma Turai

Matar Aure Ta Koma Cizon Yatsa Bayan Ta Siyar Da Kadarorinta Ta Koma Turai

  • Wata mata ƴar Najeriya da iyalanta sun ci bashin maƙudan kuɗaɗe da siyar da kadarorinsu domin fatan samun rayuwa mai kyau idan sun koma ƙasar waje
  • A yayin da su ke a UK, matsala ta fara lokacin da ta gano cewa tana buƙatar sai ta nemi izni kafin ta fara yin aiki
  • Tarin matsaloli sun yi mata yawa da suka haɗa da masu bin ta bashi daga Najeriya, biyan kuɗin makaranta, da ɗaukar ɗawainiyar yara guda biyar

Wata mata mai amfani da suna (@gloriaotikor1) ta bayar da labarin wasu ƴan Najeriya da suka shiga halin tasku a UK bayan sun ciyo bashin miiyoyin naira da siyar da gidansu da mota domin komawa ƙasar waje.

Iyalan sun koma UK ne ta hanyar yin amfani da bizar karatu wacce mahaifiyar yaran ta samu.

Kara karanta wannan

Abun Mamaki: Wata Amarya Ta Sha Mamaki Yayin da Aka Sace Mata Riga a Tsakiyar Titi

Yan Najeriya sun koma cizon yatsa bayan komawa UK
Iyalan dai sun siyar da komai da suka mallaka domin komawa UK Hoto: iStock, Shutterstock, BBC
Asali: TikTok

Bayan sun isa ƙasar wajen, sai ta fahimci cewa tana buƙatar sai ta sake neman wata biza wacce za ta ba ta damar yin aiki bayan ta kammala karatu, wacce tana da matuƙar tsada.

A cewar labarin waɗanda suka ba ta bashin kuɗi daga nan gida Najeriya sun yi ta kiranta, suna tunanin cewa da ta isa za ta biya su bashin da ta ci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar aure ta koma cizon yatsa bayan ta koma UK

Mijinta wanda yake aiki, da kyar yake iya ɗaukar nauyinsu saboda kuɗin haya da kuɗin abincin da yaran za su ci.

Duk da cewa ta ci bashin kuɗi, matar ta kasa kammala biyan kuɗin makarantar ta a ƙasar waje.

A yayin da take ba ƙawarta labarinta, matar ta bayyana cewa da ta san haka abubuwan su ke, da ba ta koma ƙasar waje ba.

Kara karanta wannan

'Yar Kwallon Najeriya Asisat Oshoala Ta Bayyana Yadda Mahaifinta Zai Ji Kan Cire Rigar Da Ta Yi Don Murna

Mutane sun yi sharhi akan bidiyon

Evolak ya rubuta:

"Samun rayuwa mai kyau ba a ƙasar waje ba ne. Inda Allah ya kaɗɗaro maka nan ne rabonka, mutane su san wannan ko sun huta da wahala."

flikky ya rubuta:

"Meyasa za su taho da yara biyar su ma a lokaci, nawa ooo."

peaches ta rubuta:

"Wannan shi ne dalilin da ya sanya na ke cewa gwara Canada da UK ta ɓangaren karatu."

user5122196360123 ya rubuta:

"Tafiyar taren da suka yi shi ne kuskurensu. Kamata ya yi su tafi ɗaya bayan ɗaya."

Kyakkyawar Baturiya Na Neman Mijin Aure

A wani labarin kuma, wata kyakkyawar baturiya ta bazama neman mijin aure ido rufe, bayan ta daɗe ba ta da saurayi.

Kyakkyawar baturiyar ta bayyana cewa a shirye take ta yi na'am da tayin soyayyar duk wanda ya shirya, ba tare da la'akari da abun hannunsa ba ko kalar fatarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng