Ya Cika Mako: Budurwa Ta Ba da Labarin Yadda Ta Kare Bayan Ziyartar Saurayinta
- Wata budurwa ta caccaki saurayinta kan yadda ya nuna mata halin ko in kula lokacin da ta kai masa ziyara a jihar Lagos
- Ta ce sun shafe shekaru uku suna soyayya da saurayin nata amma ko kudin magani bai bata ba lokacin da take jinya
- Ta kara da cewa ko sisi bai shiga tsakaninsu ba, bugu da kari babu kudin mota, haka ta dawo gida hannu rabbana
Jihar Lagos - Wata budurwa a Najeriya ta koka kan yadda tayi tafiya mai dogon zango daga Jos har jihar Lagos don kai ziyara wurin saurayinta.
Ta bayyana saurayin nata a matsayin mutum mai mako bayan ta share kwanaki a gidansa amma ko kudin mota ma bai bata ba.
Ta ce lokacin da take gidan nasa, ta kwanta jinya kuma ita tayi wa kanta magani da kudinta tun da saurayin bashi da niyyar taimakonta.
A bayaninta, ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Na ziyarci saurayina daga Jos ta jihar Plateau har Lagos, kuma ni na biya kudin mota, bayan na isa, ya tarbeni cikin fara’a."
Ta fadi damuwarta akansa
Ta ce matsalarta da saurayin shine, duk lokacin da tace tana son cin kifi ko shawarma sai yace ta kawo kudin don babu kudi a wurinsa, ta ba shi ya siyo musu amma zai fi ta ci da yawa.
Ta kara da cewa:
“Na kwanta rashin lafiya a gidansa, ni nake siya wa kai na magani har lokacin da zan tafi, ko sisi bai bani ba don na yi kudin mota, mutumin da yake ta rokona in kawo masa ziyara.
“Bayan na koma gida ko kirana bai yi ba a waya, kuma munyi soyayya har na tsawon shekaru 3, aiki ne ya kai shi Lagos, irin halin da ya nunamin ya na dauremin kai.s”
Ban San Aikin Mahaifina Ba: Faifan Bidiyon Wani Hamshikin Uba Ya Karade Kafar Sada Zumunta
A wani labarin, Wani matashi dan Najeriya ya wallafa wani faifan bidiyo na TikTok da ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta bayan da ya ce mahaifinsa yana cikin alfarma, amma bai san aikin da yake yi ba.
Yaron mai suna Daniel East Coast ya daura faifan bidiyon mahaifinsa cikin shigan alfarma da wata dankareriyar mota mai tsada lokacin da yake shirin fita zuwa aiki.
Asali: Legit.ng