A kama sana'a: Mata ta kammala digiri da 1st class, ta ba da mamaki da fara sana'ar kitso

A kama sana'a: Mata ta kammala digiri da 1st class, ta ba da mamaki da fara sana'ar kitso

  • Theresah Adusei ta kammala karatun digiri da sakamako mafi kyau a Jami'ar Ghana, kuma a yanzu tana sana'ar gyaran gashi bayan shafe shekaru tana fafutukar neman aiki
  • Matar ta yanke shawarar mayar da abin da take sha'awa ya zama kasuwanci bayan kokarinta na samun kyakkyawan aiki ya zama yasar teku kofi
  • Adusei ta kammala karatu daga jami'a, inda ta karanta Ilimin Ilimi da Ilimin bayanai da halayyar dan adam amma yanzu tana aiki a masana'antarta ta gyara gashi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ghana - Duk da cewa Theresah Adusei ta kammala karatun digiri da sakamakon '1st class' fannin ilimin bayanai da halayyar dan adam a Jami'ar Ghana, ta sha fama domin ganin ta samu aiki.

A 2019, ta sanya kanta da danginta alfahari a lokacin da ta kammala jami’a da lambar yabon karramawa, amma a yanzu burinta na samun kyakkyawan aiki ya zama tamfar yasan teku da moda.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

A wata hira da tayi da Joy Prime, Adusei ta bayyana cewa ta fara fafutukar neman aikin ta ne a lokacin da ta kusa kammala hidimar kasa.

Matar da ta kammala digiri ta koma sana'ar kitso
Sana'a sa'a: Bayan kammala digiri da 1st class, budurwa ta ba da mamaki da sana'ar kitso | Hoto: Joy News
Asali: UGC

Hakonta bai cimma ruwa ba

Ta gaya wa Joy Prime cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na fara fafutukar neman aiki, amma kana aika CVs amma ba za a sake neman ka ba."

Adusei ta sha neman taimakon manyan mutane da dama, ciki har da fastonta, da su taimaka mata wurin samun aiki mai kyau, amma hakonta bai cimma ruwa ba.

Yadda ta shiga gyaran gashi

Bayan ta shafe shekaru tana neman aiki ba tare da wani haske ba, matar mai digiri 1st class ta yanke shawarar mayar da abin da ta ke sha’awa ya zama sana’a kuma yanzu tana aikin gyaran gashi domin tallafa wa kanta da ’yan’uwanta.

Adusei ta tuna cewa:

Kara karanta wannan

Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

"Lokacin da nake jami'a, na kasance gyara gashina da kaina, kuma na kan yi wa abokan zama na. Sun taimake ni wajen gano wannan baiwar."

Ba kowa ne ke goyon bayan shawarar Adusei na shiga wannan sana’a ba, har da rashin jituwar da mahaifiyarta ta samu dafarko, amma mace mai azama kamarta, ta samu ci gaba sosai a harkar.

Kamar yadda Joy News ta ruwaito, wata shida kenan da yanzu da matar ta fara gina shagon gyaran gashi a wata kwantena tare da taimakon mahaifinta da wasu kawayenta.

Kalli bidiyon:

Na fece, yallabai: Wasikar murabus din wani ta girgiza jama'a a kafar intanet

A wani labarin, idan ka taba aiki na kwana daya a rayuwar ka kuma ka bari, to tabbas watakila ka taba rubuta takardar murabus dinka cikin salon da aka saba dashi.

Wani kuma ya zo da salo, ya mika takardar murabus dinsa mai kalmomi uku masu sauki wadanda suka bar jama'ar soshiyal midiya baki bude.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kamfanonin Jiragen Sama a Najeriya Za Su Tsayar Da Aiki Saboda Tsadar Man Jirgin Sama

Rayuwar aiki dai na da wahala. Don haka, lokacin da kake da shugaba mai ba ka wahala ko yanayin aiki mara dadi, sha'awar yin murabus a kowace rana wani abu ne da ka iya zuwa kwakwalwarka.

p

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.